Zamfara na jiran ganin matakin da rundunar soji za ta dauka kan sojan da ke kai wa yan bindiga kayayyaki

Zamfara na jiran ganin matakin da rundunar soji za ta dauka kan sojan da ke kai wa yan bindiga kayayyaki

- Gwamnatin Zamfara ta ce tana nan tana zuba ido don ganin matakin da rundunar soji za ta dauka kan jami'inta da aka kama

- An dai kama jami'in sojan ne yana kai wa yan bindiga makamai da kayayyakin sojoji

- Sai dai har zuwa yanzu hedkwatar tsaro bata ce uffam ba a kan batun

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce tana jiran matakin da rundunar soji za ta dauka a kan wani jami’in Soja da aka kama tare da budurwarsa suna bai wa ’yan fashi bindigogi da kakin sojoji.

Mataimakin shugaban Ma’aikatan gwamnati, Dr. Bashir Muhammad Maru ya ce, Sojoji ne suka kama Jami’in Sojan da budurwar tasa, jaridar Punch ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar da malaman Kano: Babu hannunmu a hana zaman, gwamnatin Kano

Zamfara na jiran ganin matakin da rundunar soji za ta dauka kan sojan da ke kai wa yan bindiga kayayyaki
Zamfara na jiran ganin matakin da rundunar soji za ta dauka kan sojan da ke kai wa yan bindiga kayayyaki Hoto: @GuardianNigeria
Asali: UGC

Maru ya ce, "Wani batu mai mahimmanci shi ne kame wani jami'in Soja da budurwarsa da ke taimakawa 'yan fashi da kakin sojoji da alburusai da aka yi kwanan nan tare da sauran masu zagon kasa.

“Yayin da gwamnatin jihar ke jiran matakin da sojoji za su dauka a kan wannan lamarin tare da yin bayani a hukumance, ci gaban ya kara tabbatar da matsayin Gwamna Bello Matawalle na cewa matukar dai ba a tsarkake yakin da ake yi da‘ yan bindiga daga bara-gurbi da masu zagon kasa ba, ba za mu samu nasarar da ake so ba a yakin”.

Lokacin da aka tuntube ta, Hedkwatar Tsaro ta yi alkawarin bayar da sanarwa kan kamun amma ba ta yi hakan ba har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton.

KU KARANTA KUMA: Ana tattaunawa da shugabannin 'yan bindiga don kawo zaman lafiya a Niger

A baya mun ji cewa 'Yan bindiga da suka addabi jihar Zamfara galibi ana ganinsu cikin kakin sojoji da muggan makamai.

Gwamnatin Zamfara ta ce an kama wani jami’in Sojan Najeriya da ke ba da alburusai da kakin soja ga ‘yan bindiga a jihar, TheCable ta ruwaito.

A wani taron manema labarai a ranar Juma'a, Bashir Maru, mataimakin shugaban ma'aikata na gwamna Bello Matawalle, gwamnan jihar, ya ce sojoji sun kame jami'in tare da budurwar sa, bayan bayanan sirri da aka samu daga al'umma.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel