Jerin sunaye: BUK ta fara karatun digiri a sabbin kwasa-kwasai 8

Jerin sunaye: BUK ta fara karatun digiri a sabbin kwasa-kwasai 8

- Jami'ar Bayero ta Kano ta bullo da sabbin kwasa-kwasai guda takwas da suka hada da na injiniya, kimiyya da sauransu

- Sanarwar da jami'ar ta fitar ya ce za a fara digiri kan sabbin kwasa-kwasan ne a zangon karatu na 2020/2021

- Jami'ar ta ce ta samu sahalewar Hukumar Kula ta Jami'o'i ta Kasa, NUC kafin fara sabbin kwasa-kwasan

Jami'ar Bayero da ke Kano, BUK, za ta fara karatun digiri a sabbin kwasa-kwasai takwas da za a fara a zangon karatu na 2020/2021.

Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da jami'ar ta aike wa Daily Nigerian a ranar Juma'a.

Jerin sunaye: BUK ta fara karatun digiri a sabbin kwasa-kwasai 8
Jerin sunaye: BUK ta fara karatun digiri a sabbin kwasa-kwasai 8. Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

Za a fara sabbin kwasa-kwasan ne bayan samun sahalewar Hukumar Kula ta Jami'o'i ta Kasa, NUC.

Wannan matakin yana cikin manyan batutuwan da aka amince da su yayin taron Majalisar Jami'ar karo na 384 da aka yi a ranar Laraba 24 ga watan Fabrairu.

DUBA WANNAN: Wike: Ni nayi addu'a kada a samu tsaro a Nigeria saboda abinda Buhari ya yi wa Rivers a 2016

Sabbin kwasa-kwasan digirin da za a fara sun hada da;

1. B.Eng Automative Engineering (Injiniya da ya shafi tsari da ƙera ababen hawa)

2. Ba.Sc Environmental Health (Digiri Lafiyar Muhalli)

3. B.Sc Taxation (Digiri a kimiyyar karbar haraji)

4. B.Sc Forensic Science (Digiri da ya shafi amfani da kimiyya don gano masu laifi)

5. DVM (Digiri a likitancin dabbobi)

KU KARANTA: Rayyuka 13 sun salwanta sakamakon harin da ƴan bindiga suka kai a Sokoto

6. B.A. (Ed) Primary Education (Digiri a ɓangaren ilimin frimare)

7. B.A. Early Childhood Education (Digiri a ɓangaren ilimin ƙananan yara)

8. B.Sc Meteorology (Digiri a kimiyyar yanayi)

Wadannan na daga cikin sabbin sauye-sauyen da shugaban jami'ar Farfesa Sagir Adamu Abbas ya ɓullo da su kamar yadda sanarwar kai ɗauke da sa hannun Hajiya Amina Umar Abdullahi, Direktan sashin jarabawa, ɗaukan sabbin dalibai da ajiye bayanai.

A wani rahoton daban kunji cewa kungiyar musulmi ta Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta ce ba za ta hallarci mukabala da gwamnarin jihar Kano ta shirya da Sheikh Abduljabbar Kabara ba, Daily Trust ta ruwaito.

An shirya yin mukabalar ne a ranar 7 ga watan Marisa tsakanin malaman Kano da Sheikh Abduljabbar da ake zargi yana yi wa Annabi Muhammad batanci cikin karatunsa.

JNI, da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ke shugabanta, ta ce bata da masaniya kan matakan da aka dauka kawo yanzu don warware rashin fahimtar

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel