A karon farko, Fafaroma Francis ya ziyarci Iraki ya rokawa Iraki zaman lafiya

A karon farko, Fafaroma Francis ya ziyarci Iraki ya rokawa Iraki zaman lafiya

- A karo na farko, Fafaroma Francis ya kai ziyara har kasar Iraki, yanki mai hatsarin gaske

- Fafaroma ya nuna jin dadinsa da shiga kasar tare da siffanta kasar da kashin bayan al'umma

- Ya kuma rokawa kasar zaman lafiya da kawo karshen ta'addanci da zaman lafiya naki daya

Fafaroma Francis ya yi kira da a kawo ƙarshen tashin hankali da ta'addanci yayin ziyarar mutum irinsa na farko a kasar Iraki, BBC Hausa ta ruwaito.

Fafaroman na yin ziyarar ce a karon farko tun bayan barkewar annobar cutar korona a duniya.

Da yake jawabi bayan Shugaban Iraƙi Barham Salih ya tarbe shi, Fafaroma ya ce ya ji dadin zuwa kasar ta Iraki wadda ya siffanta da "kashin bayan al'umma".

KU KARANTA: Ci gaba: Masana a Najeriya sun kirkiri allurar rigakafin COVID-19, saura gwaji kan mutane

A karon farko, Fafaroma Francis ya ziyarci Iraki ya rokawa kasar Iraki zaman lafiya
A karon farko, Fafaroma Francis ya ziyarci Iraki ya rokawa kasar Iraki zaman lafiya Hoto: The Guardian
Asali: UGC

"Ina addu'ar Allah ya kawo karshen makamai...Allah kawo karshen tashin hankali da ta'addanci da kungiyanci da kuma rashin hakuri da juna!" in ji shi.

"Iraki ta sha fama da yaki da ta'addanci da fakan kabilanci akasari saboda tsattsauran ra'ayi, wadanda ke hana mutane su zauna da juna cikin kwanciyar hankali."

Cutar korona da kuma matsalolilin tsaro sun sa wannan ziyara tasa ta zama mafi hadari, sai dai dattijon mai shekara 84 ya hakikance cewa "aikinsa ya je yi".

KU KARANTA: Cin hanci da rashawa zan yaka ba mutane ba, shugaban EFCC Abdurrasheed Bawa

A wani labarin, Masarautar Saudiyya ta umarci maniyyata da su yi allurar rigakafin COVID-19 gabanin aikin Hajjin na 2021, in ji jaridar Okaz.

Masarautar ta bakin Ministan Kiwon Lafiya, Tawfiq al-Rabiah, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin din da ta gabata, Aljazeera ta ruwaito.

Ministan ya ce "Alurar rigakafin ta COVID-19 wajibi ne ga wadanda suke son zuwa aikin Hajji kuma zai kasance daya daga cikin manyan sharudda (na karbar izinin zuwa)."

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel