Kotu ta dakatar da muƙabalar da aka shirya yi da Sheikh Abdul-Jabbar a Kano

Kotu ta dakatar da muƙabalar da aka shirya yi da Sheikh Abdul-Jabbar a Kano

- Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da mukabalar da ta yi shirin yi tsakanin Sheikh Abdul-Jabbar Nasir Kabara da malaman jihar Kano a ranar Lahadi

- Hakan ya biyo bayan umurnin da wata kotun Majistare da bada ne na dakatar da mukabalar bisa bukatar da wani lauya mai zaman kansa ya shigar a kotun

- Lauyan, Barrister Ma'aruf Yakasai ya ce yin mukabalar tamkar sabawa umurnin da kotu ta bada a baya ne na hana Sheikh Abdul-Jabbar yin karatu a Kano

Wata kotun Majistsare da ke zamanta Gidan Murtala a jihar Kano ta bada umurnin dakatar da mukabalar gwamnatin jihar ta shirya yi tsakanin Sheikh Abdul-Jabbar da malaman Kano a ranar Lahadi 7 ga watan Maris, BBC ta ruwaito.

Alkalin kotun, mai shari'a Muhammadu Jibrin ya yanke hukuncin dakatar da mukabalar sakamakon bukatar da wani lauya mai zaman kasan, Barrister Ma'aruf Yakasai ya shigar wa kotun.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Buhari ya bada umurnin a bindige duk wanda aka gani da AK-47

Kotu ta dakatar da muƙabalar da aka shirya yi da Sheikh Abdul-Jabbar a Kano
Kotu ta dakatar da muƙabalar da aka shirya yi da Sheikh Abdul-Jabbar a Kano. Hoto: @daily_trust
Asali: UGC

Yakasai ya bukaci a dakatar da yin mukabalar ne saboda hakan ya saba umurnin da kotu ta bayar a baya na hana Sheikh Abdul-Jabbar yin karatu da saka karatunsa a kafofin watsa labarai na jihar Kano.

Mai shigar da karar ya ce bashi daman yin magana yayin mukabalar tamkar watsa karatunsa ne wadda tunda farko aka dakatar da hakan.

KU KARANTA: Harin Boko Haram: Sojoji ba su arce daga filin daga ba, Rundunar Soji

A bangarenta, gwamnatin jihar Kano ta bada tabbacin cewa za ta yi wa kotu biyaya inda kwamishinan sharia na jihar Kano, Barrister Musa Lawan ya sanar da cewa ba za a yi mukabalar da aka shirya yi a ranar Lahadin ba.

Lauyan Barrister Ma'aruf mai suna Barrister Lukman Auwalu Abdullah ya ce hukuncin da kotun ta yanke ya musu dadi.

A wani rahoton daban kunji cewa kungiyar musulmi ta Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta ce ba za ta hallarci mukabala da gwamnarin jihar Kano ta shirya da Sheikh Abduljabbar Kabara ba, Daily Trust ta ruwaito.

An shirya yin mukabalar ne a ranar 7 ga watan Marisa tsakanin malaman Kano da Sheikh Abduljabbar da ake zargi yana yi wa Annabi Muhammad batanci cikin karatunsa.

JNI, da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ke shugabanta, ta ce bata da masaniya kan matakan da aka dauka kawo yanzu don warware rashin fahimtar

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel