Abubuwa 11 da ya kamata ku sani game da sabon Mai Tangale

Abubuwa 11 da ya kamata ku sani game da sabon Mai Tangale

- A makon nan ne gwamnan jihar Gombe ya sanar da nadin sabon Mai Tangale Sanusi Maiyamba

- Mun tattaro muku abubuwa masu muhimmanci da ya kamata ku sani game da sabon sarkin

- A baya kafin nadin, rikici ya barke yayin da aka kashe mutane da kuma asarar dukiyoyi da dama

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, a ranar Laraba ya sanar da nadin Malam Danladi Sanusi Maiyamba, a matsayin Mai Tangale na 16, Daily Trust ta ruwaito.

An fidda da sanarwar ne kwanaki 52 bayan rasuwar Dr Abdu Buba Maisheru II, Mai Tangale na 15.

Ga abubuwa 11 da ya kamata ku sani game da sabon Mai Tangale da aka nada:

1. An haifi Malam Danladi Sanusi Maiyamba a ranar 12 ga watan Fabrairun shekarar 1966 a karamar hukumar Billiri ta jihar Gombe.

Abubuwa 11 da ya kamata ku sani game da sabon Mai Tangale
Abubuwa 11 da ya kamata ku sani game da sabon Mai Tangale Hoto: Fore Front Ng
Asali: UGC

2. Ya yi karatun matakin farko na firamare a makarantar firamare ta Billiri inda ya sami takardar shedar kammala karatun matakin farko a shekarar 1979.

3. Ya yi sakandare a makarantar sakandaren kwana ta gwamnati dake barikin soja a Yola, daga shekarar 1979 zuwa 1984 don samun shedar kammala makarantar sakandare.

4. Haka nan kuma ya halarci kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya, da ke Bauchi don samun shedar kammala karatunsa a fannin harkokin mulki.

KU KARANTA: Makiyaya 2 da suka bata sun gamu da ajalinsu a Zangon Kataf

5. Ya kasance tsohon dalibi ne a Kwalejin Gudanarwa ta Ma’aikatan Najeriya (ASCON) dake Legas, inda ya samu takardar shedar kammala a fannin Gudanar da Ma'aikata a shekarar 2013.

6. Sabon Mai Tangale yana da kimanin shekaru 34 yana aikin gogewa a aikin gwamnati da ya shafi ma’aikatu da sassa daban-daban.

7. Ya yi aiki a Ma'aikatar Ilimi ta jihohin Bauchi da Gombe tsakanin 1987 zuwa 1996.

8. Tare da kirkirar jihar Gombe daga jihar Bauchi a shekarar 1996, ya dawo Gombe ya yi aiki da hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar ta Gombe daga shekarar 1996 zuwa 2004 da kuma ma'aikatar lafiya tsakanin 2004 da 2005.

9. An tura shi Kotun daukaka kara ta Shari’a dake Gombe kuma ya yi aiki tsakanin 2005 da 2011. Ya kuma kasance a Hukumar Kula da Ma’aikatun Kananan Hukumomi daga 2011 zuwa 2016

10. Tsakanin 2016 da 2021 ya kasance a Ma'aikatar Kula da Kiwo da Makiyaya tsakaninin 2016 zuwa 2018 da Hukumar Kula da Ayyukan Majalisar Dokoki ta Gombe daga 2018 zuwa 2021.

11. Maiyamba yana da aure tare da yara.

KU KARANTA: Saudiyya: Dole ne duk wanda zai zo aikin Hajji yayi allurar rigakafin COVID-19

A wani labarin, Gwamnan Gombe Muhammadu Yahaya ya nada sabon Mai Tangale, Daily Trust ta ruwaito.

An bayyana nadin Danladi Sanusi Maiyamba a ranar Laraba. Ana sa ran za a kawo karshen takaddamar da ta biyo bayan kan sarautar gargajiya ta Mai Tangale a garin Billiri dake Gombe.

Kwamishina, a Ma’aikatar kananan hukumomi da harkokin Masarauta, Ibrahim Jalo ya isar da amincewar Gwamnan kuma ya gabatar da nadin daga baya ga sabon Mai Tangle a Poshiya dake Billiri.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel