Da dumi-dumi: Gwamnan jihar Gombe ya nada sabon Mai Tangale

Da dumi-dumi: Gwamnan jihar Gombe ya nada sabon Mai Tangale

- Bayan kwantar da tarzomar rikicin Billiri, gwamnan Gombe ya nada sabon Mai Tangale

- Gwamnan ya tabbatar da nadin Danladi Sanusi Maiyamba a matsayin Sarkin garin Billiri

- An bayyana hakan a matsayin kokarin kwantar da rikicin da ya kunno kai a garin na Billiri

Gwamnan Gombe Muhammadu Yahaya ya nada sabon Mai Tangale, Daily Trust ta ruwaito.

An bayyana nadin Danladi Sanusi Maiyamba a ranar Laraba.

Ana sa ran za a kawo karshen takaddamar da ta biyo bayan kan sarautar gargajiya ta Mai Tangale a garin Billiri dake Gombe.

Kwamishina, a Ma’aikatar kananan hukumomi da harkokin Masarauta, Ibrahim Jalo ya isar da amincewar Gwamnan kuma ya gabatar da nadin daga baya ga sabon Mai Tangle a Poshiya dake Billiri.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Sowore a kotu tare da wani mai tsaron da ba a saba gani ba

Da dumi-dumi: Gwamnan jihar Gombe ya nada sabon Sarkin Tangale
Da dumi-dumi: Gwamnan jihar Gombe ya nada sabon Sarkin Tangale Hoto: The Sun News
Asali: UGC

Ya ce nadin Maiyamba ya tabbata ne ta hanyar duba da halayensa da dacewarsa.

Bikin gabatarwar ya samu halartar Shugaban karamar hukumar Billiri, Sarakuna tara na masarautar Billiri, mambobin majalisar gargajiya da sauran masu rike da mukamai.

Mai Tangale na 15, Abdu Maisharu II, ya mutu yana da shekaru 72 bayan gajeriyar rashin lafiya.

Biyo bayan mutuwar sarkin, rikici ya balle tare da nuna rashin amincewar kiristocin yankin na nada sabon sarkin da zai kasance musulmi.

An kashe mutane uku tare da lalata dukiya ta miliyoyin nairori a karamar hukumar Billiri ta jihar Gombe yayin da rikici kan nadin sabon Mai Tangale ya kara kamari.

KU KARANTA: EFCC ga 'yan Najeriya: Kada ku sake taya Bawa murnar zama shugaban EFCC

A wani labarin, Mai martaba Sarkin Karaga na jihar Neja, Alhaji Salihu Tanko ya rasu, The Nation ta ruwaito. Tsohon Sanatan Kaduna, @ShehuSani ya tabbatar da rasuwar Sarkin a shafinsa na twitter a ranar Talata.

Ya ce, “Na samu labarin bakin ciki game da rasuwar Sarkin Kagara na Jihar Neja, Alhaji Salihu Tanko. Allah Ya ba shi gidan Aljanna firdausi. Amin. Inna lillahi wainna Illayhir rajiun.”

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel