Makiyaya 2 da suka bata sun gamu da ajalinsu a Zangon Kataf

Makiyaya 2 da suka bata sun gamu da ajalinsu a Zangon Kataf

- Dakarun sojoji sun gano gawarwakin wasu makiyaya da suka bata kwanaki kadan da ska gabata

- Rundunar ta kuma kama wasu mutane tara da ake zargi da hannu dumu-dumi wajen aikata kisan

- An mika wadanda ake zargin ga hukumar 'yan sanda ta jihar Kaduna domin ci gaba da bincike

Dakarun Operation Safe Haven sun gano gawarwakin wasu makiyaya biyu da suka bata a karamar hukumar Mabuhu-Wawan Rafi da ke karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Laraba ya bayyana makiyayan da suka mutu Yusuf Ahmadu da Mustapha Bako wadanda tun farko aka bayyana cewa sun bata.

A cewar kwamishinan, makiyayan sun fita ne domin kiwo da shanunsu sannan kuma sun kasa komawa zuwa mazauninsu, The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA: EFCC ga 'yan Najeriya: Kada ku sake taya Bawa murnar zama shugaban EFCC

Makiyaya 2 da suka bata sun gamu da ajalinsu a Zangon Kataf
Makiyaya 2 da suka bata sun gamu da ajalinsu a Zangon Kataf Hotto: Punch News
Asali: UGC

Ya kara da cewa, “daga karshe an gano shanun suna ta yawo a yankin ba tare da kulawa ba tare da wasu raunukan harbin bindiga. An gano gawar makiyayan jim kadan.”

“Gwamna Nasir El-Rufai ya lura da rahotannin cikin bakin ciki, kuma ya aike da ta’aziyya ga dangin makiyayan, tare da yin addu’o’in neman hutun rayukansu.

“Ya umarci hukumomin tsaro da su tabbatar sun gudanar da cikakken bincike game da mutuwar su. Ana ci gaba da bincike kan lamarin,” in ji sanarwar.

A halin yanzu, Kwamandan ya bayyana cewa sojoji sun kuma kama mutane tara da ake zargi da hannu a mummunan harin a karamar hukumar Zangon Kataf da ke jihar.

A wani bayanin na daban, kwamishinan ya lura cewa sojojin na 'Operation Safe Haven' sun bayyana hakan a cikin rahoton aikin su da suka gabatar ga gwamnatin jihar.

Ya ce: “Idan za a tuna cewa 'yan fashi da makami sun kai hari a kauyen da yammacin ranar Lahadi, inda suka kashe mutane biyar, kamar yadda aka ruwaito a cikin wani rahoton tsaro a ranar Litinin.

“An kama mutane tara da ake zargi bayan binciken da rudunar sojojin suka yi. An gano nau'ukan makamai daga dabar.

“Gwamna Nasir El-Rufai ya karbi rahoton tare da godiya, kuma ya yaba wa sojojin kan wannan namijin kokarin da suka yi, yana mai kira ga hukumomin tsaro da su tabbatar da sun hukunta wadanda ake zargin."

Ya kara da cewa "An mika wadanda ake zargin ga 'yan sanda don ci gaba da bincike,"

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Gwamnati ta amince da biyan N797.2bn na aikin hanyar Abuja-Kaduna-Kano

A wani labarin, Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo a ranar Laraba ya nanata cewa jihar ba za ta bayar da filaye kyauta don kiwo ba, yana mai cewa kiwo kasuwanci ne na kashin kai, Channels Tv ta ruwaito.

Gwamnan ya fadi hakan ne a cikin wasu sakonni da ya wallafa a shafin sa na Twitter yayin da yake karin bayani kan wani bayani da ya gabatar a baya game da shirin sauya fasalin kiwon dabbobi a yayin taron tsaro da aka gudanar a ranar Litinin.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel