Wani matashi dake bautar ƙasa yaci ƙyautar sabuwar mota

Wani matashi dake bautar ƙasa yaci ƙyautar sabuwar mota

- Wani matashi dake bautar ƙasa a jihar neja ya ci kyautar dalleliyar mota daga Access Bank

- Matashin ya nuna matuƙar farin cikinsa don a cewarsa baitaɓa tsammanin wannan nasarar ba.

- Yi amfani da manhajar bankin (app) da kuma hanyar wayoyin hannu (USSD)

Access Bank ya bayyana wani matashi mai suna Tolulope Agbaje, a matsayin wanda ya lashe kyautar da bankin yasa ma kostomoninsa.

Matashin dake aikin bautar kasa (NYSC) a jihar Niger ya bayyana tsantsar farin cikinsa da wannan nasara da ya samu.

Agbaje, yaci kyautar sabuwar mota, Hyundai Accent, wadda aka damƙa mishi a ya yin da bankin ke bikin mika kyaututtuka ga wadanda suka sami nasara a Lagos. Kamar yadda jaridar Thenation ta wallafa.

KARANTA ANAN: Gwamnonin Arewa maso gabas sun soki aikin Mambilla, sun ce a takarda ake kwangilar

Matashin yace ya yi matukar mamakin lokacin da aka faɗa masa nasarar tasa kafin abun ya zama gaskiya.

Ya kuma yi kira ga masu amfani da banki da su bude asusu a Acces Bank domin bankin na nuna kulawarsa ga konstomominsa.

Wani matashi dake bautar ƙasa yaci ƙyautar sabuwar mota
Wani matashi dake bautar ƙasa yaci ƙyautar sabuwar mota hoto: @Officialnyscng
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Kwalelenku: Alkali bai ba EFCC damar karbe wasu gidajen Bukola Saraki da ake ta shari'a a kansu ba

A bayanin da matashin yayi lokacin da aka damƙa mishi motar yace: "Har yanzun ina cikin mamaki domin ban taɓa tsammani ba"

"Bazan iya tuna adadin mu'amalar da nayi da bankin ba, amma nasan nayi dayawa sosai. Ban taɓa tsammanin mallakar mota a shekaru uku masu zuws ba amma Access bani ita," a cewar matashin

Daraktan bankin mai kula da hulɗar jama'a, Mr. Victor Etuokwu, yace an shirya wannan kyautar ne domin masu mu'amala da bankin.

Daraktan ya bayyana cewa, sun duba mu'amala 10 ne da matashin yayi yasa suka zabesa suka bashi wannan kyautar.

A jawabinsa, manajan bankin mai kula da mu'amaloliin bankin ta yanar gizo, Osakwe Edwards, yace wannan shirin zai bunkasa yin amfani da bankin ta wayoyin hannu da yanar gizo.

Yakuma kara da cewa Agbaje, ya samu wannan nasarar ne bayan an zabesa daga cikin wasu kostomonin.

Yace akwai miliyoyin mutane da sukayi kwatankwacin abin Agbaje yayi, amma shine ya kasance wanda aka zaba daga karshe.

Ya kuma bayyana cewa, wannan itace mota ta 3 da bankin ya bayar kyauta ga kwastomansa.

A wani labarin kuma Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana babban sirrinsa na haddar Alqur'ani

Dahiru Bauchi yace tun daga iyayensa ne suka samo sirrin haddar daga kabilar Bare-bari a Borno Amma daga bisani bayan zuwan Sheikh Inyass, ya roka wa mutane saukin haddar Alkur'ani

Ahmada Yusuf na da burin samun nasarori a fannin jarida.

Za'a iya samunsa a twitter @ahmadyusufmuha77

Asali: Legit.ng

Online view pixel