Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana babban sirrinsa na haddar Al-Qur'ani

Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana babban sirrinsa na haddar Al-Qur'ani

- Dahiru Bauchi yace tun daga iyayensa ne suka samo sirrin haddar daga kabilar Bare-bari a Borno

- Amma daga bisani bayan zuwan Sheikh Inyass, ya roka wa mutane saukin haddar Alkur'ani

- Shehin malamin yace yara masu shekaru bakwai ko biyar cikin sauki suke haddace Alkur'ani

Babban malamin darikar Tijjaniya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bayyana sirrinsa na haddar Al-Qur'ani mai girma.

Kamar yadda malamin ya sanar da BBC Hausa a wata tattaunawa da tayi da shi, ya ce suna da wani sirri da iyayensu suka samo na hadda daga Borno wajen kabilar Bare-Bari.

"Daga baya yayin da Sheikh Ibrahim Inyass ya bayyana, ya roki Allah da ya bada karamar haddar Alkur'ani. Hakan ne yasa aka huta nemo maganin karatun Alkur'ani. Shehu ne ya riga ya rokawa mutane kuma ake hadda cikin sauki," a cewarsa.

KU KARANTA: Yadda jiragen sama ke wurgawa 'yan bindiga makamai da abinci a Zamfara

Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana babban sirrinsa na haddar Al-Qur'ani
Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana babban sirrinsa na haddar Al-Qur'ani. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

"Za ka iya samun yaro mai shekaru 7 a duniya ko kuma mai shekaru 5 ya haddace Alkur'ani," in ji Shehin malamin.

Babban shehin malamin ya sanar da cewa yayi karatuttuka masu yawa amma wanda yake da shaida kansa shine haddar Alkur'ani da tafsirinsa. Ya ce hatta manyan malaman tafsirin sun tabbatar da iyawarsa.

KU KARANTA: Da duminsa: Buhari ya bukaci a tsananta tsaro a iyakokin tudun kasar nan

A wani labari na daban, wasu 'yan bindiga sun kai samame a yankin Kwaita da ke Kwali a babban birnin tarayya a Abuja inda suka harbe mace mai juna biyu kuma suka tisa keyar mutum 3 da suka hada da mijinta.

Wani mazaunin yankin wanda ya bukaci a boye sunansa, ya sanar da Daily Trust cewa lamarin ya faru ne wurin karfe 11 na daren Laraba.

Ya ce masu garkuwa da mutanen sun kutsa gidajen inda suka kwashesu yayin da suka dinga harbe-harbe. Ya ce harsashin da aka harba ne ya samu matar mai juna biyu.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel