Kwalelenku: Alkali bai ba EFCC damar karbe wasu gidajen Bukola Saraki da ake ta shari'a a kansu ba
- Hukumar EFCC ta koma kotu da tsohon shugaban majalisa, Dr. Bukola Saraki
- Alkali bai yarda jami’an EFCC su karbe gidajen Saraki da ke Ikoyi ba tukuna
- EFCC na karar tsohon Gwamnan ya saye gidajen ne daga baitul-malin Kwara
Alkali mai shari’a a babban kotun tarayya da ke Legas, Liman Mohammed, ya yi watsi da karar da aka shigar da tsohon shugaban majalisa, Dr. Bukola Saraki.
Hukumar EFCC ta bukaci a ba ta dama ta karbe wasu gidajen Bukola Saraki har abada. A ranar Alhamis, 5 ga watan Maris, 2021, Alkalin ya cigaba da shari’a.
Jaridar Daily Trust ta ce Mai shari’a Liman Mohammed ya ki karbar karar da EFCC ta ke yi a kan tsohon shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki.
Rahoton ya ce kotun tarayyar ba ta amince da bukatar EFCC na karbe gidajen ‘dan siyasar masu lamba No. 17 da 17A a kan layin Donald, unguwar Ikoyi, Legas, ba.
KU KARANTA: An wawuri N800m a fadar Oba a lokacin da zanga-zangar #EndSARS
A karshen zaman da aka yi a jiya, sai dai Alkali Liman Mohammed ya karbi hujjojin da aka gabatar da baki. Saraki ya yi farin ciki da hukuncin da aka zartar.
Hakan na zuwa ne bayan lauyan EFCC Nnaemeka Omewa da mai kare Saraki a kotu, Kehinde Ogunwumiju (SAN), sun gabatar wa kotu da matsayarsa a rubuce.
A baya, kotu ta bada umarni a rike wadannan gidaje saboda gudun wanda ake tuhumar ya saida su a kasuwa, a karshe hakan zai jawo wa EFCC da gwamnati asara.
EFCC ta na ikirarin da kudin haram aka saye wadannan gidaje lokacin da Saraki yake gwamna a Kwara. Tsohon gwamnan ya ce sharri kurum hukumar ta ke yi masa.
KU KARANTA: Hake-haken ma’adanai ya haddasa rashin zaman lafiya a Zamfara
Bukola Saraki ya ce ya na sa rai tun da wannan shari'a ta zo karshe ba tare da EFCC ta yi nasara ba, a daina yi masa sharri, a kyale shi ya yi rayuwarsa a Najeriya.
A jiya ne ku ke fahimtar tsuguno ba ta kare ga tsohon shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu ba.
Wani mutum da ya bada shaida a kotu ya ce akwai hannun Ibrahim Magu a badakalar Abdulrasheed Maina wanda ake zargi da wawurar kudin fansho.
Wannan shaida ya ce EFCC ta yi gaba da gidaje 222 da PRTT ta karbe. Ana zargin Magu da sharara karya, da karya rantsuwar da ya yi a lokacin ya bayyana a Majalisa.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng