Gwamnonin Arewa maso gabas sun soki aikin Mambilla, sun ce a takarda ake kwangilar
- Gwamnonin Arewa maso gabas sun sake yin zama ranar Alhamis a Jihar Bauchi
- Kungiyar gwamnonin sun yi tir da yadda ake gudanar da aikin wutan Mambila
- A cewar gwamnonin yankin, wannan aiki ya na tafiya ne kurum a kan takarda
Gwamnonin jihohin Arewa maso gabas sun yi taro a makon nan, inda su ka tattauna game da wasu matsalolin da su ka addabi yankin na su.
Daily Trust ta ce wadannan gwamnoni sun koka a game da halin da ake ciki a kan aikin wutar lantarkin Mambilla Hydroelectric Power Project
A cewar gwamnonin na Arewa ta gabas, wannan kwangilar wutar lantarki a takarda kurum ta tsaya.
Ana aikin Mambilla hydropower project da zai samar da karfin lantarki 3.05GW daga ruwa ne a rafin Dongo a kauyen Kakara, da ke jihar Taraba.
KU KARANTA: Gwamnoni zasu tattauna kan yadda za a raba rigakafin COVID-19
A takardar da gwamnonin su ka fitar bayan taron da su ka yi ranar Alhamis a jihar Bauchi, sun yi kira ga gwamnatin tarayya ta duba kwangilar.
Gwamnonin sun ce wannan aikin wuta na Mambila ya na da tasirin canza halin da yankin da ma Najeriya ta ke ciki idan aka samu aka kammala.
Mai girma gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum shi ne ya sa hannu a wannan matsaya da aka cin ma a matsayinsa na shugaban kungiyar.
Haka zalika kungiyar gwamnonin ta koka cewa an zalunci bangaren Arewa maso gabas a kason manyan ayyuka da gwamnati tarayya za ta yi a 2021.
KU KARANTA: Ibo za su fara noma domin su huta gorin mutanen Arewa
Zulum da sauran takwarorin na sa sun gode wa gwamnatin tarayya na zaben wasu tituna a yankin, a matsayin wadanda Dangote da Ashaka su gyara.
Shekaru 40 kenan da gwamnati ta bada kwangilar wutar Mambilla amma har yau shiru ake ji.
An fara bada kwangilar wannan aiki ne a 1973, a 2007 gwamnatin Obasanjo ta sake tado da maganar, sai kuma Marigayi Umaru Yar’adua ya soke kwangilar.
Daga baya an sake kakakkabe takardun wannan aiki, aka ce za a karkare komai a 2012. Bayan nan sai aka kai gwamnati a kotu, nan maganar ta tsaya sai yanzu.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng