Idan da Sheikh Gumi Kirista ne, da gwamnatin Buhari ta yi Allah wadai da kalamansa, sannan ta kame shi, CAN

Idan da Sheikh Gumi Kirista ne, da gwamnatin Buhari ta yi Allah wadai da kalamansa, sannan ta kame shi, CAN

- Kungiyar CAN ta yi martani a kan kalaman da aka alakanta da Sheikh Ahmed Gumi

- CAN ta ce da ace shugaban Kirista ne ya yi wannan furuci da tuni jami'an tsaro sun gayyace shi sannan fadar Buhari ta fito tayi Allah-wadai da shi

- Ta kuma bayyana shirun Shugaba Buhari a matsayin yarda da kalaman Shehin malamin

Kungiyar Kiristocin Najeriya ta nuna damuwarta cewa shirun da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi na tsawon lokaci game da wasu maganganun kwanan nan da shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi ya yi, yana nufin amincewa da ikirarin nasa.

Daya daga cikin irin wadannan ikirarin na Gumi shi ne cewa sojoji kirista su ne ke kashe barayi da masu tayar da kayar baya a kasar.

Kungiyar kiristocin ta yi kira ga Gumi da ya janye "kalaman rashin kishin kasa da rarrabuwa" da aka alakanta da shi domin neman zaman lafiya da hadin kan kasar.

Idan da Sheikh Gumi Kirista ne, da gwamnatin Buhari ta yi Allah wadai da kalamansa, sannan ta kame shi, CAN
Idan da Sheikh Gumi Kirista ne, da gwamnatin Buhari ta yi Allah wadai da kalamansa, sannan ta kame shi, CAN Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

A cikin wata sanarwa a ranar Laraba, 3 ga watan Maris, CAN ta ce shirun da Shugaban ya yi yana nufin yarda da maganganun Gumi, Sahara Reporters ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun afka gidan kwamishinan Sakkwato, sun sace mutum biyu

Sanarwar wacce babban sakataren CAN din, Joseph Daramola, ya sanya wa hannu ya ce, “Idan wani ya ce sojojin Kirista ne ke kai hari ga 'yan bindiga, wannan mutumin ba ya fatan kasar nan da alheri kuma ba ya son yaki da ta'addanci da' yan ta'adda ya ƙare cikin nasara.

“Ba za a iya ɗaukar hujjar murya ta Gumi da muhimmanci ba saboda ana iya shirya shaidar sautin murya da gangan don kafa hujja. Abu na biyu, ta yaya za mu iya tabbatar da amincin mutumin da ke zargin cewa sojojin Kirista ne ke kai hari ga garuruwa da 'yan fashi?

“Wannan ikirarin da bai dace ba, baya ga bacin rai da raba kan rundunar sojin Najeriya da zai yi gida biyu ta bangarn addini, zai kuma bata martabar sojojin da ba kirista ba a matsayin wadanda basu jajirce wajen yaki da ta’addanci ba.

“Shirun da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi na tsawon lokaci daidai yake da amincewa da furucin Gumi mai hadari. Idan da za a danganta abin da Gumi ya fada ga shugaban kirista, da jami'an tsaro sun gayyace shi ko kuma su bayyana shi a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo, kuma da Fadar Shugaban kasa ta yi Allah wadai da wannan shugaban na Kirista.

KU KARANTA KUMA: Dan adaidaita sahu ya mayar da N2.8m ga fasinja bayan ya tsinci kudin a cikin adaidaitarsa

“Mun tuna yadda jami’an tsaro suka yi da kalaman Suleiman, Dr Obadiah Mailafia, Prophet Isa El-Buba da kuma na baya-bayan nan, Shugaban Katolika Dr Matthew Hassan Kukah sannan gwamnati ma ta yi martani. Shin da gaske muna da tsarkakkun da ba a tabawa a kasar yanzu?”

A gefe guda, Kungiyar matasan Ibo ta 'The Ohanaeze Ndigbo Youth Council, OYC,' ta bukaci a kama malamin addinin musulunci da ke kokarin yin sulhu da yan bindiga a arewacin Najeriya, Sheikh Ahmad Gumi nan take, rahoton PM News.

Gumi ya fusata kungiyar ta Igbo ne sakamakon kwatanta shugaban Ibo, marigayi Dim Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu da yan bindiga a hirar da aka yi da shi a BBC Pidgin.

Ojukwu ne ya jagorancin kabilar Ibo yayin yakin basasar Nigeria da aka shafe shekaru uku ana gwabzawa wadda ta yi sanadin salwantar miliyoyin rayyuka, kuma na ganin laifin da Ojukwu ya yi ta yi kama da na yan bindiga.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel