Kungiyar Ibo ta buƙaci a kama Sheikh Ahmad Gumi a bincike shi

Kungiyar Ibo ta buƙaci a kama Sheikh Ahmad Gumi a bincike shi

- Kugiyar The Ohanaeze Ndigbo Youth Council, OYC, ta yi kira ga hukumomin tsaro su kama Sheikh Ahmad Gumi sun bincike shi

- Kungiyar ta furta hakan ne bayan Gumi ya kwatanta yan bindiga da marigayi tsohon jagorar Ibo Dim Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu

- Kungiyar ta OYC ta ce duba da yadda Gumi ke kokarin kare yan bindigan yana cewa su ba yan ta'adda bane, ya kamata a bincike shi

Kungiyar matasan Ibo ta 'The Ohanaeze Ndigbo Youth Council, OYC,' ta bukaci a kama malamin addinin musulunci da ke kokarin yin sulhu da yan bindiga a arewacin Najeriya, Sheikh Ahmad Gumi nan take, rahoton PM News.

Gumi ya fusata kungiyar ta Igbo ne sakamakon kwatanta shugaban Ibo, marigayi Dim Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu da yan bindiga a hirar da aka yi da shi a BBC Pidgin.

DUBA WANNAN: An kuma: 'Yan bindiga sun sake garkuwa da fasinjoji 50 a Neja

Ohaneaze: Kungiyar Ibo ta bukaci da damke Sheikh Ahmad Gumi
Ohaneaze: Kungiyar Ibo ta bukaci da damke Sheikh Ahmad Gumi. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Ojukwu ne ya jagorancin kabilar Ibo yayin yakin basasar Nigeria da aka shafe shekaru uku ana gwabzawa wadda ta yi sanadin salwantar miliyoyin rayyuka, kuma na ganin laifin da Ojukwu ya yi ta yi kama da na yan bindiga.

A martaninsa, Mazi Okwu Nnabuike, Shugaban OYC na kasa, ya ce ya yi mamakin yadda har yanzu hukuma ba ta kama Gumi ba.

Ya ce duk da cewa akwai alamun Gumi na da 'alakar soyayya' da yan ta'addan, jami'an tsaro sun kawar da kansu sun bar shi yana yawo yayinda tsaro ke cigaba da tabarbarewa a kasar.

OYC cikin sanarwar da ta raba wa manema labarai ta ce, "Nigeria na kan gaba a tarihinta na cigaba da zama kasa daya. Ba a taba samun lokacin da ake tafka laifuka a kasar nan ba da sunan kungiyoyi bayan daban-daban.

KU KARANTA: Kuma dai, Ƴan bindiga sun sace ɗalibai 3 a jihar Katsina

"Abinda ya fi tada hankali shine yadda mai magana da yawun yan ta'addan, Sheikh Gumi ke yawonsa duk da cewa ana iya gani karara yana cikin matsalolin tsaron Nigeria.

"Ya fara da ikirarin cewa yan bindiga ba yan ta'adda bane, sannan ya kwatanta yan bindiga da IPOB yanzu kuma yana kwantanta su da Dim Odumegwu Ojukwu, babu shakka Gumi ya zama kakakin yan ta'adda don haka a kama shi a bincike shi."

Sanarwar ta kara da cewa dama ba yau ya fara furta maganganu da kan iya raba kan kasa ba da tada zaune tsaye don haka ta yi kira ga jami'an tsaro su kama shi su bincike shi don haka ne kadai hanyar kawo karshen kashe-kashe da garkuwa da mutane.

A wani labarin daban, kun ji Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi, NDLEA, ta kama wani mai fataucin miyagun kwayoyi mai shekaru 36 dauke da hodar Iblis da ta kai na Naira biliyan daya.

NDLEA ta ce mai safarar, Nkem Timothy, wanda ya yi basaja a matsayin Auwalu Audu domin yin fataucin kunshin hodar Iblis da nauyinsa ya kai 1.550kg. An yi kiyashin kudinsa ya kai Naira biliyan 1.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin da ya ke kokarin zuwa Algeria ta bodar jamhuriyar Nijar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel