Dan adaidaita sahu ya mayar da N2.8m ga fasinja bayan ya tsinci kudin a cikin adaidaitarsa

Dan adaidaita sahu ya mayar da N2.8m ga fasinja bayan ya tsinci kudin a cikin adaidaitarsa

- Guled Ibrahim ya fahimci cewa wata mata ta bar makudan kudade a cikin adaidaita sahunsa sannan ya fara neman ta

- Kuɗin mallakar ɗaya daga cikin fasinjojinsa ne, wata mahaifiya mara lafiya da ya sauke a asibiti tare da ɗanta

- Direban adaidaita sahun ya isa asibiti ya tarar tuni ta tafi bayan ta yi kuka game da halin da take ciki

An karrama wani matashi saboda gaskiyarsa bayan ya dawo da KSh 815k (N2,827,437.35) ga wata mata mara lafiya wacce ta batar da shi a cikin abar hawarsa.

Guuled Ibrahim ya sauke wata uwa da danta a asibiti a Jigjija, Habasha, inda suka je neman lafiya.

A cewar Mustafa Omer, mataimakin shugaban karamar hukuma ta Somaliya a Habasha - wanda ya yada labarin a Facebook, daga baya sai uwar ta fahimci cewa babu jakar da ke dauke da kudin.

Dan adaidaita sahu ya mayar da N2.8m ga fasinja bayan ya tsinci kudin a cikin adaidaitarsa
Dan adaidaita sahu ya mayar da N2.8m ga fasinja bayan ya tsinci kudin a cikin adaidaitarsa Hoto: Mustafa Omer/ Deputy chief's office.
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Yanzun-nan: Jihohin kudu 6 sun yi martani a kan hana abinci daga arewa, sun bayyana matakin dauka na gaba

Bayan ta sayar da dabbobinta don tara kudin asibitin dan nata, matar da abin ya rutsa da ita ta kwashe tsawon awanni tana kuka amma daga baya ta bar asibitin.

Daga baya Guled ya fahimci cewa matar da ya sauke ta manta kudinta a cikin TukTuk sannan ya garzaya asibiti don neman uwar mara lafiyar.

Mustafa ya rubuta:

"Ba da daɗewa ba aka yi kiran waya aka ga matar; an kawo ta asibiti kuma an mayar mata da kuɗin. Ta sake yin kuka: wannan karon cikin farin ciki."

Mataimakin shugaban ya ce ya kamata a daukaka irin wannan labarin wanda ke nuna mutuntaka da ladabi tare da karrama shi a tsaka da duk wani mummunan labari.

A cewar jaridar Ethiopian Today, Mustafa ya gayyaci mutanen biyu zuwa ofishinsa kuma ya godewa Guled da danginsa, sannan ya kara da cewa abubuwan da ya aikata sun nuna kyakkyawan sunan yankin.

Matashin direban, wanda rahotanni suka ce ya bar jami’a don tallafa wa danginsa, ya ce abin da ya yi ya samo asali ne daga kyakkyawar tarbiyyar da ya samu.

KU KARANTA KUMA: Daga karshe Gwamna Matawalle ya bayyana wadanda ke daukar nauyin 'yan ta'adda a Zamfara

Gwamnatin ta sha alwashin tallafawa Guled don ya kammala karatunsa da fatan zai iya samar da ayyukan yi a nan gaba.

A wani labarin, Kungiyar matasan Ibo ta 'The Ohanaeze Ndigbo Youth Council, OYC,' ta bukaci a kama malamin addinin musulunci da ke kokarin yin sulhu da yan bindiga a arewacin Najeriya, Sheikh Ahmad Gumi nan take, rahoton PM News.

Gumi ya fusata kungiyar ta Igbo ne sakamakon kwatanta shugaban Ibo, marigayi Dim Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu da yan bindiga a hirar da aka yi da shi a BBC Pidgin.

Ojukwu ne ya jagorancin kabilar Ibo yayin yakin basasar Nigeria da aka shafe shekaru uku ana gwabzawa wadda ta yi sanadin salwantar miliyoyin rayyuka, kuma na ganin laifin da Ojukwu ya yi ta yi kama da na yan bindiga.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel