Jam'iyyar APC da PDP sun shiga musayar yawu akan korar da Ganduje ya yiwa Dawisu

Jam'iyyar APC da PDP sun shiga musayar yawu akan korar da Ganduje ya yiwa Dawisu

- Bayan kwanaki biyu hannun DSS, an saki Salihu Tanko Yakassai (Dawisu)

- Gabanin haka, gwamna Ganduje ya sallamesa daga matsayinsa na hadimin kafafen yada labarai

- Manyan yan siyasa irinsu Fayose da Sule Lamido sun yi tsokaci kan haka

Jam'iyyar mai mulki APC da kuma babbar Jam'iyyar adawa ta PDP sun fara musayar kalamai akan korar tsohon mai bada shawara ta musamman akan yada labarai, Salihu Tanko Yakasai, da gwamna Ganduje yayi.

Gwamna Ganduje na Jihar Kano ya kori Yakasai ne bisa rashin Da'a da tuhuma da yakewa Jam'iyya mai mulki APC.

A rahoton da jaridar dailytrust ta wallafa, mataimakin shugaban Jam'iyyar APC na rikon kwarya a wani sako daya turawa jaridar yace, korarren mai taimakawa gwamnan ya saba magana ne akan ra'ayin wasu wanda da yawan su yan jam'iyyar hamayya ce ta PDP.

KU KARANTA: Dillalan shanu sun shiga hannun DSS saboda hana kai kaya Kudancin Najeriya

Jam'iyyar APC da PDP sun shiga musayar yawu akan korar da Ganduje ya yiwa Dawisu
Jam'iyyar APC da PDP sun shiga musayar yawu akan korar da Ganduje ya yiwa Dawisu Hoto: @dawisu
Asali: Twitter

KU DUBA: Babu sasanci tsakaninmu da 'yan bindiga, Gwamnatin Kaduna ta jaddada

"Idan ba aiki yake musu ba, taya shi korarren mai taimakawa gwamanan zaiyi raga raga da shugabancin Jam'iyya a dukkan matakai? Ba sai an fada ba, jam'iyyar APC mai mulki ta cimma abubuwa da dama haka zalika mafi yawancin gwamnoni da yan majalisu," yace.

Ya kuma kara da cewa "daya daga cikin misalin dake nuna haka shine sabon mahallin Yakassai, saboda haka muna goyon bayan Gwamna."

Amma a daya bangaren kuma, shugaban jam'iyyar PDP na jihar kano, Shehu Sagagi yace, mai yuwuwa Yakasai na fadin ainihin abinda ke cikin ransa ne da na mai gidansa Gwamna Ganduje.

Wannan bashi ne karon farko da Salihu Yakasai ke sakin baki irin wannan ba.

Kun ji cewa hukumar yan sandan farar hula, SSS, ta sako Salihu Tanko Yakasai Dawisu tsohon mai magana da yawun gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Yayan Salihu Yakasai, Umar, ne ya tabbatar wa Daily Nigerian hakan a daren ranar Litinin.

"Yanzu DSS ta sako dan uwa na. Muna hanyar mu ta zuwa gida yanzu," ya ce ba tare da karin bayani game da sharrudan belin ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel