Labari da ɗuminsa: SSS ta sako Salihu Tanko Yakasai Ɗawisu
- Hukumar ta SSS ta sako tsohon hadimin gwamna Ganduje na jihar Kano, Salihu Tanko Yakasai
- Hukumar yan sandan farar hular da kama Tanko Yakasai ne tun a ranar Juma'a kan wani laifi da kawo yanzu bata bayyana ba
- Dan uwan Salihu Yakasai, Umar ya tabbatar da sakinsa inda ya ce suna hanyar tafiya gida a daren ranar Litinin
Hukumar yan sandan farar hula, SSS, ta sako Salihu Tanko Yakasai Dawisu tsohon mai magana da yawun gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganuje, Daily Nigerian ta ruwaito.
Yayan Salihu Yakasai, Umar, ne ya tabbatar wa Daily Nigerian hakan a daren ranar Litinin.
"Yanzu DSS ta sako dan uwa na. Muna hanyar mu ta zuwa gida yanzu," ya ce ba tare da karin bayani game da sharrudan belin ba.
DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Tawagar gwamnan Bauchi ta yi haɗari, 'yan sanda 10 sun jikkata
A daren ranar Asabar ne SSS ta amsa cewa ita ce ta kama Mr Tanko Yakasai bayan jama'a sun dade suna cece-kuce kan batun a dandalin sada zumunta.
Shugaban hukumar ta SSS reshen jihar Kano, Alhassan Mohammed, da farko a safiyar ranar Asabar ya musanta cewa hukumar ne ta kama Mr Tanko Yakasai, inda ya ce rahoton jita-jita ne kawai.
KU KARANTA: 'Sau 10 aka kama ni', Tanko Yakasai ya yi martani kan tsare ɗansa
Amma cikin wata sanarwa da ya aike wa Daily Nigerian a daren ranar Asabar, kakakin hukumar, Peter Afunanya, ya tabbatar da zargin da ake yi da farko na cewa hukumar ce ta kama Dawisu.
Gabanin kama Yakasai, Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya ce ya sallami shi ne saboda 'furta maganganu' da suka ci karo da tsarin jam'iyyar APC da gwamatin jihar da ya ke yi wa aiki.
A wani labarin daban, ofishin mai bawa Shugaban Kasa shawara kan Tsaro da Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Pantami, a jiya sun sha banban kan kaddamar da fasahar sadarwa ta 5G a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.
Sun yi magana ne a Abuja yayin wani taro da kwamitocin Majalisar Dattawa kan Sadarwa, Kimiyya da Fasaha, da Yaki da Laifukan Yanar Gizo da Lafiya da Cututtuka masu Yaduwa suka shirya kan matsayin fasahar 5G.
A yayin da Pantami ya ce Najeriya ta shirya tsaf domin kaddamar da fasahar 5G, ofishin NSA ta nuna damuwarta kan wasu matsaloli da ke tattare da fasahar.
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng