Babu sasanci tsakaninmu da 'yan bindiga, Gwamnatin Kaduna ta jaddada

Babu sasanci tsakaninmu da 'yan bindiga, Gwamnatin Kaduna ta jaddada

- Gwamnatin Kaduna ta sake jaddada cewa babu sasanci tsakaninta da 'yan bindiga kwata-kwata

- Kamar yadda kwamishinan cikin gida yace, 'yan bindigan da ke barna duk daga jihohin da ke makwabtaka suka zo

- Aruwan ya sanar da hakan ne bayan harin da 'yan bindiga suka kai kananan hukumomin Zangon Kataf da Chikun

Gwamnatin jihar Kaduna ta jaddada cewa babu sasanci da zai shiga tsakaninta da 'yan bindiga duk da hauhawar miyagun ayyukansu a jihar.

Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya sanar da gidan talabijin na Channels a wata tattaunawa cewa 'yan bindigan da ke kawo hari duk daga jihohi masu makwabtaka ne, don haka babu dalilin sasanci da su.

Ya kara da yin bayanin cewa gwamnatin jihar tare da hadin guiwar ta tarayya suna aiki tukuru domin ganin sun shawo kan hare-haren da suka ta'azzara ballantana a kauyuka.

KU KARANTA: Mayakan ISWAP sun kaiwa kwamandan Operation Lafiya Dole farmaki a Borno

Babu sasanci tsakaninmu da 'yan bindiga, Gwamnatin Kaduna ta jaddada
Babu sasanci tsakaninmu da 'yan bindiga, Gwamnatin Kaduna ta jaddada. Hoto daga @Channelstv
Asali: Twitter

Tsokacin Aruwan na zuwa ne jim kadan bayan rahoton da ya fito na cewa a kalla mutum 10 aka kashe bayan 'yan bindiga sun kai hari kauyukan Zango Kataf da karamar hukumar Chikun a jihar.

Kamar yadda Aruwan yace, 'yan bindigan sun kai hari kauyen Gandu da ke karamar hukumar Zango Kataf inda suka kashe mutum biyar.

Sun kone gidaje 10, babura 2 da buhunan citta 50. Wasu manoman rani sun rasa injinan ban ruwansu tare da kayan ayyukansu.

KU KARANTA: Kagara: 'Yan bindiga basu tausayi ko tsoro, sun ce alkawarinsu gwamnati ta karya, Hauwa

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Osun kuma ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola a ranakun karshen mako ya musanta labarin da ke yawo na cewa ya samu albashinsa na watanni 96 a sirrance a lokacin da yayi shugabancin jihar.

Ya kwatanta rahoton da labarin kanzon kurege wanda aka hada shi domin zubar da nagartar Ogbeni Rauf Aregbesola.

A wata takarda da hadimin Aregbesola na yada labarai, Soka Fasure ya fitar, ya ce rahoton da ake yaduwa a yanar gizo ya saba dokokin jaridanci, The Nation ta wallafa.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel