Dillalan shanu sun shiga hannun DSS saboda hana kai kaya Kudancin Najeriya

Dillalan shanu sun shiga hannun DSS saboda hana kai kaya Kudancin Najeriya

- Biyo bayan hauhawar farashin kayan abinci a kudu, DSS ta gayyaci shugaban dillalan shanu

- Kungiyar dillalan ta bayyana cewa shugabanta na tare da DSS kuma ana tsorata su kan yajin aikin da suka shiga

- Sun shawarci gwamnati da ta kuji wani rudani da zai iya tasowa ta hanyar daina tsorata mambobinsu

Rahotanni sun bayyana irin tashin farashi na kayan abinci na naman shanu dasukayi a kudancin Najeriya biyo bayan yajin aiki da kungiyar dillalai tayi

Jagorancin dillalan Shanu da na Abinci a karkashin kungiyar Hadakar dillalan Shanu da na Kayan Abinci (AUFCDN) a halin yanzu suna tare da jami'an Ma’aikatar Gwamnati. (DSS), Daily Trust ta ruwaito.

Babban Sakatare na AUFCDN, Ahmed Alaramma, wanda ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a Labour House dake Abuja a jiya Litinin, ya ce Shugaban kungiyar, Mohammed Tahir, yana tare da DSS.

Alaramma ya kuma yi zargin cewa jami’an tsaron na tsoratar da mambobi da kuma kungiyar kwadagon, yana mai bai wa gwamnati shawara da ta guji rudani da ke shirin kunno kai ta hanyar daina tsoratar da mambobinsu.

KU KARANTA: Jihar Benue ta saki shanu 210 ga makiyaya bayan karbar tarar Naira miliyan 5

Dillalan shanu sun shiga hannun DSS saboda hana kai kaya Kudancin Najeriya
Dillalan shanu sun shiga hannun DSS saboda hana kai kaya Kudancin Najeriya Hoto: The Nation
Asali: UGC

Tun farko kungiyar dillalan ta sha alwashin ci gaba da yajin aikin na ta a fadin kasar baki daya da kuma ci gaba da aiwatar da doka kan hana kayan abinci da shanu daga shigowa yankin kudancin kasar.

Yajin aikin, a cewarsu, zai dore har sai gwamnatin tarayya ta biya musu bukatunsu, wanda suke bukatar a biyasu naira biliyan 445 na diyyar rayukan mambobi da dukiyoyin da suka yi asara a lokacin zanga-zangar #EndSARS da rikicin kabilanci na kasuwar Shasa.

KU KARANTA: COVID-19: A fara yiwa jami'an gwamnati rigakafin kafin talakawa, in ji Tomori

A wani labarin, Yajin aikin da dillalan kayan abinci suka shiga na kungiyar Hadin kan Dillalan Kayan Abinci da Shanu (AUFCDN), ya janyo hau-hawan farashin kayayyaki a yankin kudancin Najeriya, a cewar rahoton Daily Trust.

Kungiyar ta AUFCDN wacce bangare ne na kungiyar kwadago ta kasa wato (NLC), ta shiga yajin aikin ne a ranar Alhamis biyo bayan karewar wa'adin da ta bai wa Gwamnatin Tarayya na kwana bakwai da ta biya mata bukatunta.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel