Kyakkyawar 'yar Arewa ta kammala jami'a, yan Najeriya sunce kyanta kadai na iya rikitar da Alkali

Kyakkyawar 'yar Arewa ta kammala jami'a, yan Najeriya sunce kyanta kadai na iya rikitar da Alkali

  • Wata kyayyawar budurwa ta bayyana alfaharinta da wani nasara da ta samu na kammala karatu
  • Budurwar mai suna Maryam Musa ta yi murnar kammala karatun digirinta a tsangayar ilmin shari'a
  • Yan Najeriya sun taya ta murna yayinda wasu suka yi ta kalamai kan kyawun da Allah yayi mata

Yan Najeriya sun kwararawa wata budurwa sakonnin taya murna ga kyakkyawar budurwa yar Arewa bisa nasaran da ta samu.

Budurwar mai suna Maryam Musa ta yi sanarwa a shafin Tuwita bisa kammala karatun digirinta a fannin karatun lauya.

Maryam, wacce bata bayyana jami'ar da ta kammala ba ta godewa Allah bisa nasarar da ta samu.

Yan Najeriya sun jinjina mata bisa irin kyawun da Allah ya bata yayinda wasu ke taya ta murnan kammala karatunta.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi Ya Soki Sauya Takardun Kudi, Ya Kwatanta Hakan da Halaka Kai

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Budurwar ta bayyana hotunanta sanye da kayan lauyoyi.

Hakazalika wasu sun bata shawari kan rayuwa bayan karatu.

KU KARANTA: Buhari ya bukaci majalisa ta tabbatar Bawa matsayin sabon shugaban hukumar EFCC

Kyakkyawar 'yar Arewa ta kammala jami'a, yan Najeriya sunce kyanta kadai na iya rikitar da Alkali
Kyakkyawar 'yar Arewa ta kammala jami'a, yan Najeriya sunce kyanta kadai na iya rikitar da Alkali Hoto: @marymusa
Asali: Twitter

KU DUBA: Farashin litan man fetur zai iya tashi N190 yayinda farashin danyen mai ya kai $63

@AliyuIbrahimA13 yace: "Ina tayaki murna Barista. ina bukatar kyakkyawar lauya irinki, wacce za ta iya rikita Alkali."

@Mushin24789 yace; "Ki kasance mai gaskiya duk inda kika samu kanki kuma kada kiyi rashin adalci a aiki..."

@Omacares1 yace: "Allah ya cigaba da kare ki da shiryar dake hanya madaidaici bisa wannan babban nasara."

A bangare wata matashiyar budurwa a kafar sada zumuntar zamani ta twitter mai amfani da suna @ButterBibi ta janyo cece-kuce bayan ta bayyana tsabar soyayyarta ga mawaki Don Jazzy.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Buhari Ya Amince da Sauya Wasu Takardun Naira, CBN Tayi wa Ministan Martani

A wasikar da budurwar ta rubuta, ta lissafo jerin nagartattun halayen mawakin da yasa take son shi.

Ta yi dogaro da karamcinsa, kyawunsa da kuma yadda yake mutunta jama'a a matsayin abubuwan da suka sa take kaunarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel