Da Duminsa: Buhari Ya Amince da Sauya Wasu Takardun Naira, CBN Tayi wa Ministan Martani

Da Duminsa: Buhari Ya Amince da Sauya Wasu Takardun Naira, CBN Tayi wa Ministan Martani

  • Babban bankin Najeriya ya sanar da cewa ya bi dukkan matakan da suka dace kafin fara yunkurin sauya wasu takardun kudin kasar nan
  • Mai magana da yawun CBN, Osita Nwanisobi yace bankin ya aikewa Buhari wasika kuma ya aminta da a sauya kudin, yayi mamakin furucin ministan kudi a lamarin nan
  • Nwanisobi yace ba a dauka wannan matakin don muzgunawa wata kungiya ba sai don karuwar kasar da ‘yan kasa baki daya wanda yace kamata yayi ‘yan Najeriya su goyi bayansu

FCT, Abuja - Babban bankin Najeriya, CBN ta bi dukkan matakan da suka dace wurin sabunta takardun naira uku da zai yi, Daily Trust ta rahoto.

Mai magana da yawun babban bankin, Osita Nwanisobi ya sanar da hakan yayin martani ga Ministan kudi, kasafi da tsari, Zainab Ahmed, wacce tace ma’aikatar ta bata da masaniya kan sabon tsarin.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC Tayi Nasarar Daure 'Yan Damfara 2, 800 a Watanni 10 a 2022

Buhari da Emefiele
Da Duminsa: Buhari Ya Amince da Sauya Wasu Takardun Naira, CBN Tayi wa Ministan Martani. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A yayin da ta bayyana gaban kwamitin majalisar wakilai a ranar Juma’a, ministan ta soki lamarin wanda tace bai dace a wannan lokacin ba.

Amma Nwanisobi ya bayyana mamakinsa kan ikirarin ministan inda yace CBN ma’aikata ce kafaffiya kuma ta aikewa Buhari wasika kan cewa zata sauya wasu takardun Naira wanda ya amince da hakan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayi kira ga ‘yan Najeriya da su goyi bayan sauya kudaden inda yace dukkan ‘yan Najeriya zai amfana tare da jaddada cewa wasu mutane sun boye kudade masu yawa ba a ma’adanar bankunan kasuwanci ba.

Wannan yayin yace bai dace a bar shi tsakankanin ‘yan Najeriya ba da basu yi wa kasar fatan alheri.

Har ila yau, yace yanayin kula da kudi a kasar nan yana fuskantar kalubale wanda ke barazana ga nagartar kudin, CBN da kasar.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: FG Ta Nisanta Kanta da Batun Sauya Wasu Takardun Naira

Nwanisobi ya kara da cewa, CBN ta yi hakuri na tsawon lokaci don yanzu shekaru 20 kenan da ba a sake tsarin kudin kasar ba wanda ya dace a dinga hakan duk shekaru biyar zuwa takwas.

A yayin tabbatarwa da ‘yan Najeriya cewa sake tsarin wasu kudaden aikin babban bankin ne kuma ba a yi hakan don wasu kungiyoyi bane, yace kokarin zai assasa tare da takaita amfani da tsabar kudi.

Hakazalika hakan zai shawo kan matsalolin ta’addanci da garkuwa da mutane inda ake amfani da kudin dake wajen bankuna wurin biyan kudin fansa.

A don haka Nwansobi yayi kira ga ‘yan Najeriya, ba tare da duba matsayinsu ba da su goyi bayan sauya kudaden saboda amfanin kasar baki daya.

FG Ta Nisanta Kanta da Batun Sauya Wasu Takardun Naira

A wani labari na daban, Kasa da sa’o’i arba’in da takwas bayan Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya sanar da cewa bankin zai sauya wasu daga cikin kudaden kasar a ranar 15 ga watan Disamban 2022, gwamnatin tarayya a ranar Juma’a tace bata amince da hakan ba.

Ministan kudi, kasafi da tsari, Zainab Ahmed tace bata amince da tsarin ba inda tace in har aka tabbatar da shi za a samu babbar matsala a kasar da tattalin arzikinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel