Yanzu-yanzu: Buhari ya bukaci majalisa ta tabbatar da Bawa matsayin sabon shugaban hukumar EFCC
- Shugaba Buhari ya sallami Magu gaba daya, ya nada sabon shugaban EFCC
- A karon farko an nada matashi mai shekaru 40 matsayin sabon shugaban hukumar
- Hukumar EFCC na da hakkin binciken wanda ake zargi da hambadar dukiyar gwamnati da na al'umma
Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dattawa ta tabbatar da Abdulrasheed Bawa a matsayin zababben shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Talata.
DUBA NAN: Farashin litan man fetur zai iya tashi N190 yayinda farashin danyen mai ya kai $63
KU KARANTA: Kyakkyawar 'yar Arewa ta kammala jami'a, yan Najeriya sunce kyanta kadai na iya rikitar da Alkali
Bawa, dan shekara 40 ne kuma yana daya daga cikin sabbin dauka a hukumar EFCC a 2005.
Ya karbi ragamar daga hannun Mohammed Umar wanda ke mukaddashi tun watan Yulin 2020 da dakatad da Ibrahim Magu kan zargin almundahana.
Ya yi karatun digirinsa a tattalin arziki, kuma ya yi digiri na biyu a ilmin diflomasiyya.
Har ila yau, an bukaci Shugaba Muhammadu Buhari da ya gabatar da rahoton kwamitin shari’a kan tsohon Mukaddashin Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu, Premium Times ta ruwaito.
A cikin wata wasika da aka aika wa shugaban, babbar kungiyar kawancen yaki da cin hanci da rashawa ta duniya ta nuna matukar damuwar cewa an tsoma bakin siyasa a cikin aikin EFCC.
Ta kuma bayyana gazawar mahukuntan Najeriya wajen fitar da rahoton dake da alhakin faduwar Najeriya a kwanan nan a shirin yaki da cin hanci da rashawa da kungiyar Transparency International ta yi.
Asali: Legit.ng