Tsuleliyar budurwa ta rubutawa Don Jazzy wasikar soyayya ranar masoya, ta janyo cece-kuce
- Wata budurwa 'yar Najeriya ta zabi ranar masoya domin rubutawa mawaki Don Jazzy hadaddiyar wasika
- Daga cikin manyan halayensa da suka sa matashiyar budurwar ke kaunarsa akwai karamcinsa da mutunta jama'a
- Amma kuma sai dai wasu ma'abota amfani da Twitter sun zarga cewa budurwar tana kwadayin tarin dukiyarsa ne
Wata matashiyar budurwa a kafar sada zumuntar zamani ta twitter mai amfani da suna @ButterBibi ta janyo cece-kuce bayan ta bayyana tsabar soyayyarta ga mawaki Don Jazzy.
A wasikar da budurwar ta rubuta, ta lissafo jerin nagartattun halayen mawakin da yasa take son shi.
Ta yi dogaro da karamcinsa, kyawunsa da kuma yadda yake mutunta jama'a a matsayin abubuwan da suka sa take kaunarsa.
Lamarin da ya bai wa kowa mamaki shine yadda ta dora ruwa da maganin ciwon kai a kan wasikar inda tace za ta sha su idan ya ki karbar tayin soyayyarta.
KU KARANTA: 'Yan bindiga na tara kudin siyan makami mai linzami na harbo jiragen sama, Gumi
Ma'abota amfani da kafar sada zumuntar sun ce sun dauka salon budurwar kuma za su rubuta wasika ga wadanda suka hango suna kauna.
Wasu kuwa sun sha mamakin lamarin ganin cewa ba wata babba bace. Wasu cewa suka yi tsabar son abun duniya ce ta sa budurwar mika kokon bararta ga mawakin.
A wani labari na daban, Farfesa Umar Labdo sakataren kungiyar samar da cigaban Fulani ne wato FULDAN, sannan kuma farfesa ne a bangaren siyasar musulunci a jami'ar Yusuf Maitama Sule dake jihar Kano.
A wata tattaunawa da aka yi da shi ya bayyana tushen rikicin makiyaya da manoman kasar nan da kuma yadda za a shawo kan lamarin.
Kamar yadda yace, "Yadda aka bai wa Fulani kwanaki su tattara kayansu ba a kyauta ba, in dai har ana neman zaman lafiya. Akwai Yarabawa da suke damfara a yanar gizo da Ibo da suke sayar da miyagun kwayoyi a jihata wacce nake zama a arewa. Kuma suna zaune lafiya sana sana'o'insu babu wanda yace su kwashe kayansu."
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng