Farashin litan man fetur zai iya tashi N190 yayinda farashin danyen mai ya kai $63

Farashin litan man fetur zai iya tashi N190 yayinda farashin danyen mai ya kai $63

- Tun da aka shiga watan Febrairu, farashin danyen mai ya tashi akalla sau biyu a kasuwar duniya

- Hakan na nufin cewa farashin litan mai zai hau a gidajen man Najeriya

- Kungiyoyin kwadaga na yiwa gwamnatin barazana kan shirin kara farashin

Masu ruwa da tsaki a sashen man feturin kasar nan na shawara kan sabon farashin litan man fetur yayinda farashin danyen mai ya haura $63 ga ganga a kasuwar duniya ranar Litinin.

A yanzu dai ana sayar da litan man fetur ne tsakanin N159 da N165 a gidajen mai a fadin tarayya, amma wannan farashin zai iya haurawa N190 a kwanakin nan yayinda farashin da mai ke shigowa Najeriya yau N180 daga N151 sakamakon tashin farashin danyen mai a kasuwar duniya.

Tashin farashin danyen mai daga $58 zuwa $63 a jiya na nufin cewa kudin masu tace danyen mai zai karu wajen saya, tafiyarwa da kai mai ga kwastamomi.

Hakazalika kudin da yan kasuwan mai suke kashewa zai karu kuma zasu daura wannan kari kan jama'an Najeriya.

A makon da ya gabata, kungiyoyin kwadago, yan siyasan adawa da kuma yan Najeriya sun yi kira ga gwamnati kada ta sake kara farashin man fetur.

KU DUBA: Buhari ya bukaci majalisa ta tabbatar Bawa matsayin sabon shugaban hukumar EFCC

Farashin litan man fetur zai iya tashi N190 yayinda farashin danyen mai ya kai $63
Farashin litan man fetur zai iya tashi N190 yayinda farashin danyen mai ya kai $63 Credit: @NNPCgroup
Asali: UGC

DUBA NAN: Kyakkyawar 'yar Arewa ta kammala jami'a, yan Najeriya sunce kyanta kadai na iya rikitar da Alkali

A baya mun kawo muku cewa karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Cif Timipre Sylva ya gargadi ‘yan Nijeriya da su kasance cikin shirin jure wahalar karin farashin mai yayin da farashin danyen mai ya haura sama da $60 a kowace ganga..

Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin Inganta Kudin Najeriyar a ranar Talatar da ta gabata, Sylva ya ce ba tare da samar da tallafi a cikin kasafin kudin 2021 ba, Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC), ba zai iya ci gaba da daukar nauyin da ke kasa-kasa ba.

A cewar Ministan, yayin da kudaden shigar da gwamnati ke samu ya inganta ta hanyar hauhawar farashin danyen mai, ba za a iya damunta cikin biyan tallafi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng