'Yan bindiga na tara kudin siyan makami mai linzami na harbo jiragen sama, Gumi
- Malamin musuluncin nan, Ahmad Gumi ya bayyana yadda 'yan bindiga suke sarrafa kudaden fansar da suke amsa
- A cewarsa, suna tattara kudaden ne don su siya makami mai linzami na harbo jiragen sama
- A wata tattaunawa aka yi dashi ya bayyana hakan, inda yace ya kamata gwamnati ta yafe musu laifukansu
Ahmad Gumi, babban malamin addinin nan, ya ce 'yan bindiga suna tattara kudaden da suke amsa a matsayin kudaden fansa daga hannun jama'a don siyan makami mai linzami na harbo jiragen saman.
Gumi ya samu ganawa da wasu 'yan bindiga a dajin jihar Zamfara.
Bayan ganawar ne ya bukaci gwamnatin tarayya ta yafe musu ta kuma taimaka musu, don sun rasa shanunsu sakamakon rikicin nan.
KU KARANTA: Ku wasa takubbanku domin yaki: APC ga magoya bayanta na Kano kafin zuwan zabe
A tattaunawar da The Punch suka yi da Gumi, ya ce da yuwuwar ta'asar 'yan bindiga ta karu idan gwamnati bata yi wani abu ba a kai.
Gumi ya ce 'yan bindiga sun fi sojoji sanin lunguna da sakunan dake cikin dajikan, don haka za su yi amfani da wannan damar wurin cutar dasu, shiyasa ya shawarci gwamnati da ta sasanta dasu.
"Wadannan sune mutanen da suka fara fuskantar satar shanu, masu satar shanu da bindigogi sun raba su da shanunsu. Daga nan ne suka fara siyan makamai sai kuma garkuwa da mutane. Yanzu suna siyan miyagun makamai wadanda zasu iya tarwatsa jirgi. Wannan babban tashin hankali ne wanda yakamata a dakatar," cewar Gumi.
"Idan aka yafe musu, za su ajiye makamansu. Sai aje a gina musu makarantu da asibitoci don zamansu lafiya ya tabbata.
"Indai da bindiga ne babu yadda za a yi dasu. Saboda sun fi sojojinmu sanin lunguna da sakunan dake dajin. Don haka gara a sasanta dasu."
KU KARANTA: Za a iya samun kwanciyar hankali bayan rabuwa, zubar da kiyayya ake yi, Rahama Indimi
Malamin ya ce akwai wasu jami'an tsaron da suke kai wa 'yan bindiga labarai.
"Suna da magoya baya ko ina, har cikin jami'an tsaro. Wani daga cikinsu ya ce basu da manyan motocin da za su tafi da shanu, kuma basu da mayanka, don haka akwai mutanen da suke hada kai dasu. Ko garkuwa da mutanen da suke yi wasu ne suke sanar dasu masu kudin anguwanni," a cewarsa.
A wani labari na daban, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce tubabben sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, bai fahimci nauyin da ke kan shugabannin gargajiya ba, musamman shugaba irin na babbar masarauta irin ta Kano.
Ganduje ya fadi hakan ne a wata tattaunawa da gidan Talabijin din Channels suka yi da shi. Inda suka bukaci sanin dalilan da suka sanya ya tube wa sarkin rawaninsa lokacin yana kan karagar sarautar Kano.
A cewar Ganduje, "Tubabben sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, bai fahimci rawar da shugabannin gargajiya ya kamata su dinga takawa ba."
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng