Za a iya samun kwanciyar hankali bayan rabuwa, zubar da kiyayya ake yi, Rahama Indimi

Za a iya samun kwanciyar hankali bayan rabuwa, zubar da kiyayya ake yi, Rahama Indimi

- Diyar biloniyan nan na Maiduguri, Rahama Indimi ta ce za a iya samun zaman lafiya bayan ma'aurata sun rabu

- Ta yi wannan furucin ne a ranar Alhamis, tana tsaka da farin cikin samun babbar nasara akan Mohammed Babangida a kotu

- A cewar Rahma, sau uku tsohon mijinta yana kai ta kotu don ya samu ya amshi yaransu, sai dai kuma ko yaushe nasara take samu

Diyar wannan biloniyan na Maiduguri, Rahma Indimi ta ce akwai yuwuwar samun kwanciyar hankali da zaman lafiya tsakanin ma'aurata bayan sun rabu.

Matar mai yara 4 ta bayyana hakan a ranar Alhamis, bayan kwana biyu da samun nasararta a kotu, Shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

A cewar Rahma, sai da tsohon mijinta, Mohammad Babangida, ya maka ta kotu har sau uku don ya samu a bashi damar rike su, amma ita take ta nasara.

KU KARANTA: Rashin tsaro: A haramtawa makiyayan kasashen ketare shigowa kasar nan, Ganduje

Za a iya samun kwanciyar hankali bayan rabuwa, zubar da kiyayya ake yi, Rahama Indimi
Za a iya samun kwanciyar hankali bayan rabuwa, zubar da kiyayya ake yi, Rahama Indimi. Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

"Tsohon mijina ya kai ni kotu don a bashi damar rike yaranmu, amma na yi nasara. Alhamdulillah. Karo na uku kenan," kamar yadda ta bai wa wani amsa da ya tambayeta a kafar sada zumunta ta Instagram.

A shafinta ta bayyana wani tsokaci da tayi a Instagram, inda tayi godiya mara misaltuwa ga wadanda suka ba ta goyon baya. Ta shawarci zawarawa da su dinga maka tsofaffin mazajensu a kotu don su amshi yaransu.

"Nagode sosai. Nagode da kwarin guiwar da ku ka bani. Ya kamata mutane su gane cewa ana samun natsuwa bayan rabuwar aure. Ba komai bane na fada. Tabbas idan ka sake aure, za a yi ta yada maganganu iri-iri."

"Maza ko mata, kada ku dinga fada da junanku. Ku dinga iyakar kokarinku don zaman lafiya yaranku. Kada ku yarda ku dinga fada gaban yaranku, ku ajiye tsana da sauransu."

KU KARANTA: Sojin Najeriya basu son ganin karshen ta'addanci saboda suna amfana da shi, Sheikh Gumi

A wani labari na daban, ofishin sifeta janar na 'yan sanda zai gurfanar da tsohon gwamnan jihar Imo, Ikedi Ohakim, a gaban kotu a ranar Litinin, 15 ga watan Fabrairu bisa laifin tozarta wata Chinyere Amuchinwa.

Kamar yadda TheCable ta ruwaito, za a gurfanar da tsohon gwamnan ne tare da wani Chinedu Okpareke gaban Taiwo Taiwo, alkalin babbar kotun tarayya, bisa laifuka 5 wadanda suke da jibi da yanar gizo.

An kama Okpareke amma an sake shi bayan ya cika sharuddan beli.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel