Muhammadu Sanusi II bai san nauyin da ke kan sarakuna ba, ya cika surutu, Ganduje

Muhammadu Sanusi II bai san nauyin da ke kan sarakuna ba, ya cika surutu, Ganduje

- Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya ce tubabben sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II bai fahimci nauyin da ke kan shugabannin gargajiya ba

- Ganduje ya ce kalubalantar gwamnati ba laifi bane, amma duk wanda ya samu kan shi a wuri toh dole ya sauya tsarin rayuwarsa

- Ya ce Sunusi mutum ne mai ilimi, kuma mai caccakar gwamnati a koyaushe don ba a kan gwamnatinsa ya fara ba, tun lokacin da Kwankwaso yana gwamna ya taba

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce tubabben sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, bai fahimci nauyin da ke kan shugabannin gargajiya ba, musamman shugaba irin na babbar masarauta irin ta Kano.

Ganduje ya fadi hakan ne a wata tattaunawa da gidan Talabijin din Channels suka yi da shi. Inda suka bukaci sanin dalilan da suka sanya ya tube wa sarkin rawaninsa lokacin yana kan karagar sarautar Kano.

A cewar Ganduje, "Tubabben sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, bai fahimci rawar da shugabannin gargajiya ya kamata su dinga takawa ba.

KU KARANTA: Rashin tsaro: A haramtawa makiyayan kasashen ketare shigowa kasar nan, Ganduje

Muhammadu Sanusi II bai san nauyin da ke kan sarakuna ba, ya cika surutu, Ganduje
Muhammadu Sanusi II bai san nauyin da ke kan sarakuna ba, ya cika surutu, Ganduje. Hoto daga @ChannelsTv
Asali: Twitter

"Tabbas tubabben sarkin kullum cikin caccaka da sukar gwamnati yake, kuma ba laifi bane yin hakan saboda kowa yana da damar tofa albarkacin bakinsa. Tabbas mutum ne mai ilimi kwarai.

"Bari in baka wani misali, lokacin ina mataimakin gwamna, muna mulkar jihar tare da gwamna Rabiu Musa Kwankwaso, Sunusi darektan wani banki ne a lokacin. Kuma ya yi wani furuci wanda bai yi wa gwamnati dadi ba.

"A lokacin ya caccaki aikin da gwamnati take yi, inda yace maimakon a samar da ruwa a jihar Kano, muna can muna gina gida a Abuja. Kuma gidan masaukin baki ne amma na gwamnatin jihar Kano ne a Asokoro.

"Ya ce maimakon yadda muke gyara tituna don mutane suji dadin tafiya, mai zai hana mu gina makarantu. Ka ga wannan ai kalubalantar gwamnati yake yi.

"A gwamnati kuma ba komai ake tankawa ba, idan kace zaka biye wa mutane toh babu wani abin kirkin da zaka tsinana.

"Gwamnan Kano na lokacin ya bukaci bankin su kori Sunusi ko kuma gwamnati ta cire kudadenta da suke bankin. Bankin basu kore shi ba, don haka gwamnati ta cire kaf dukiyarta da take bankin, a lokacin N969,000,000 ba zan taba mantawa ba," a cewar gwamnan.

KU KARANTA: Zargin cin amana: PDP ta dakatar da wani shugabanta a jihar Katsina

A wani labari na daban, Gwamnann jihar Bauchi, Bala Mohammed ya ce Fulani makiyaya ya zama dole ne suke daukar makamai domin bai wa kansu kariya.

A yayin jawabi ga wani taron manema labarai wanda Chapel of Nigeria Union Journalist reshen jihar Bauchi suka yi, gwamnan ya ce wannan makaman da suke yawo da su shine yasa suke gujewa barayin shanun da ke kashe su tare da yin awon gaba da shanunsu.

Mohammed ya ce gazawar gwamnati na bai wa makiyaya kariya yasa suke bai wa kansu, Daily Trust ta ruwaito.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel