Ku wasa takubbanku domin yaki: APC ga magoya bayanta na Kano kafin zuwan zabe

Ku wasa takubbanku domin yaki: APC ga magoya bayanta na Kano kafin zuwan zabe

- Abdullahi Abbas, shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC na jihar Kano, ya bai wa 'yan jam'iyyarsa shawara

- Ya shawarci 'yan ga ni kashenin jam'iyyar da su kai wa duk wanda ya yi kokarin yin murdiyar zabe farmaki

- Ya sanar da hakan ne a ranar Juma'a a Kano yayin rantsar da ciyamomi 44 na kananun hukumomin jihar

Abdullahi Abbas, shugaban kwamitin rikon kwaryar jam'iyyar APC na jihar Kano, ya umarci duk masu kishin jam'iyyar da su kai wa duk wanda yayi yunkurin yin murdiyar zabe a jihar farmaki.

Abbas ya dade yana bai wa 'yan jam'iyyar kwarin guiwa akan siyasa. Ya ja kunnen 'yan jam'iyyar a wani taro da suka yi a watan Janairu, inda yace akwai mummunan mataki da jam'iyya za ta dauka akan duk wanda bai sake rijistar ba.

Shekarar da ta gabata, jam'iyyar ta shirya yin wani shiri na "violence for violence" akan zaben 2023, The Cable ta wallafa.

KU KARANTA: Rashin tsaro: A haramtawa makiyayan kasashen ketare shigowa kasar nan, Ganduje

Ku wasa takubbanku: APC ga magoya bayanta na Kano kafin zuwan zabe
Ku wasa takubbanku: APC ga magoya bayanta na Kano kafin zuwan zabe. Hoto daga @Thecableng
Source: Twitter

Ya yi wannan bayanin ne a taron da suka yi na rantsar da shugabannin kananun hukumomi 44 a jihar Kano, inda Abbas yace duk wanda yayi yunkurin magudin a zabe mai zuwa zai kwashi kashinsa a hannu.

"Na umarceku da ku ladabtar da duk wanda kuka gani yana kokarin satar akwatin zabe da sunan magudi. Babu abinda zai faru," kamar yadda yace.

Ya bukaci duk wasu 'yan jam'iyyar APC da suka halarci taron a Kano, da su shirya kare hakkin jam'iyyar idan zaben 2023 ya zo.

A jawabin gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya shawarci sababbin shugabannin da aka zaba da su dage kuma su zage damtse wurin yin aiki tukuru da kuma hana da cin hanci a jihar.

KU KARANTA: Da duminsa: UAE ta haramtawa 'yan Najeriya zuwa Dubai saboda Covid-19

A wani labari na daban, fitaccen malamin addinin Islama a arewacin Najeriya ya zargi rundunar sojin Najeriya da amfana da rashin tsaron da kasar nan ke ciki wanda hakan yasa basu son ta'addanci ya zo karshe sakamakon manyan kudaden da suke samu.

Sheikh Gumi, wanda yake ziyartar 'yan bindiga a dajika domin sasanci tare da tabbatar da zaman lafiya, a ranar Alhamis ya sanar da hakan yayin da aka yi hira da shi a Arise News.

"Rundunar sojin Najeriya bata bada kwarin guiwa wurin yaki da ta'addanci saboda tana matukar samu daga rashin tsaro," yace.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit.ng

Online view pixel