Da duminsa: Jami'an 'yan sanda sun mamaye Lekki toll gate dake Legas

Da duminsa: Jami'an 'yan sanda sun mamaye Lekki toll gate dake Legas

- 'Yan sanda sun mamaye Lekki toll gate da ke Legas ana jajiberin ranar da masu zanga-zanga za su fito

- Runduna ta musamman ta hukumar 'yan sandan jihar Legas ne suka tabbatar da cewa jami'an 'yan sandan sun mamye wurin

- Dama jama'a sun yi niyyar fara zanga-zangar ne bayan kotu ta amince da bukatar kara bude toll plaza

'Yan sandan jihar Legas sun tsaya tsayin daka wurin dakatar da zanga-zangar End SARS wacce matasa suka shirya farawa a ranar Asabar a Lekki toll gate.

Runduna ta musamman ta 'yan sandan jihar Legas ne suka tabbatar da dakatarwar, The Nation ta ruwaito.

"CSP Yinka Egbeyemi wanda yanzu haka ya jagoranci 'yan sanda domin tsaron Lekki Toll Gate (Admiralty Plaza) Obalende, Ikoyi, Jakande Roundabout, da wasu bangarori na Eti Osa," kamar yadda RRS suka wallafa a shafinsa na Twitter ranar Juma'a da daddare.

KU KARANTA: Sojin Najeriya basu son ganin karshen ta'addanci saboda suna amfana da shi, Sheikh Gumi

Da duminsa: Jami'an 'yan sanda sun mamaye Lekki toll gate dake Legas
Da duminsa: Jami'an 'yan sanda sun mamaye Lekki toll gate dake Legas. Hoto daga @Thenation
Source: Twitter

Hukumar 'yan sanda tana iyakar kokarin ganin ta kara baiwa jami'anta na bangarorin kwarin guiwa.

Dama an shirya yin zanga-zangar ne bayan wasu mutane 9 sun bukaci amincewar kotu don a kara bude toll plaza.

Shugaban, Alkali Doris Okuwobi da wasu mutane 4 su ne suka bukaci LCC ta kara bude wurin.

KU KARANTA: Rashin tsaro: A haramtawa makiyayan kasashen ketare shigowa kasar nan, Ganduje

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya ce Fulani makiyaya ya zama dole ne suke daukar makamai domin bai wa kansu kariya.

A yayin jawabi ga wani taron manema labarai wanda Chapel of Nigeria Union Journalist reshen jihar Bauchi suka yi, gwamnan ya ce wannan makaman da suke yawo da su shine yasa suke gujewa barayin shanun da ke kashe su tare da yin awon gaba da shanunsu.

Mohammed ya ce gazawar gwamnati na bai wa makiyaya kariya yasa suke bai wa kansu, Daily Trust ta ruwaito.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit.ng

Online view pixel