Kada ku ga laifin makiyaya idan suna yawo da miyagun makamai, Gwamnan Bauchi
- Sanata Bala Mohammed, gwamnan jihar Bauchi ya ce dole ne yasa makiyaya basu da wata mafita da ta wuce yawo da makamai
- Kamar yadda ya sanar, laifin aika-aikarsu duk ya rataya ne a wuyan gwamnati da al'umma da suka kasa basu kariya
- Gwamnan ya sanar da yadda wasu bata-gari ke tare makiyayan su kashe su tare da yin awon gaba da shanunsu
Gwamnann jihar Bauchi, Bala Mohammed ya ce Fulani makiyaya ya zama dole ne suke daukar makamai domin bai wa kansu kariya.
A yayin jawabi ga wani taron manema labarai wanda Chapel of Nigeria Union Journalist reshen jihar Bauchi suka yi, gwamnan ya ce wannan makaman da suke yawo da su shine yasa suke gujewa barayin shanun da ke kashe su tare da yin awon gaba da shanunsu.
Mohammed ya ce gazawar gwamnati na bai wa makiyaya kariya yasa suke bai wa kansu, Daily Trust ta ruwaito.
Ya ce: "Saboda makiyaya na yawo da shanu gari-gari, dole suna shiga dajika. Hakan yasa barayin shanu suke kashe su tare da yin awon gaba da dukiyarsu.
KU KARANTA: 'Yan sanda: Shanun da suka kutsa gidan Soyinka na wani bayerabe ne ba bafulatani ba
"Bashi da wata mafita da ya wuce yawo da AK47 saboda gwamnati da al'umma sun kasa basu kariya. Wannan kuwa laifin gwamnati ne da na jama'a.
“Ba za a ce wannan laifi bane domin kuwa a kowanne kabila akwai masu laifi."
KU KARANTA: Bidiyon jarumar yarinya tana fatattakar kattin 'yan fashi daga shagon mahaifiyarta da adda
A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta sanar da cewa shanun da suka kutsa cikin gidan Wole Soyinka na wani bayerabe ne.
A yayin zantawa da manema labarai a ranar Laraba, Abimbola Oyeyemi, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ya ce shanun na wani Kazeem Sorinola ne wanda ya dauka wani bafulatani wanda yake kula da shanun.
"Shanun na wani bayerabe ne mai suna Kazeem Sorinola. Ya bai wa wani bafulatani kula da shanun ne. Shanun ba na bafulatanin bane, dan tsaro ne kawai," Oyeyemi yace.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng