Rashin tsaro: A haramtawa makiyayan kasashen ketare shigowa kasar nan, Ganduje

Rashin tsaro: A haramtawa makiyayan kasashen ketare shigowa kasar nan, Ganduje

- Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya soki maganar da gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi akan rashin tsaron yankin arewa maso yamma

- Dama gwamna El-Rufai yace saboda rashin daukar matakan da suka dace da gwamnonin arewa maso yamma ne suke janyo hauhawar rashin tsaro a yankunan

- Yayin da RFI suke tattaunawa da Ganduje ya ce ba lallai El-Rufai ya fahimci kokarin da jami'an tsaro suke yi bisa umarnin gwamnonin yankinsu ba

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya soki furucin da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai yayi akan matsalar rashin tsaron yankin arewa maso yamma, Punch ta wallafa.

Idan ba a manta ba gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce rashin jajircewar gwamnonin yankin arewa maso gabas ne ya sanya kullum rashin tsaro yake hauhawa a yankin.

Sai dai a wata hira da gidan rediyon faransa (RFI) suka yi da shi a Kano a ranar Alhamis, Ganduje ya ce El-Rufai ba zai taba fahimtar kokarin da gwamnoni suke yi ba na umartar jami'an tsaro.

KU KARANTA: 'Yan sanda: Shanun da suka kutsa gidan Soyinka na wani bayerabe ne ba bafulatani ba

Rashin tsaro: A haramtawa makiyayan kasashen ketare shigowa kasar nan, Ganduje
Rashin tsaro: A haramtawa makiyayan kasashen ketare shigowa kasar nan, Ganduje. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

A cewar Ganduje, an shawarci jami'an tsaron da suke jihar Kano, Kaduna da Bauchi da su hada karfi da karfe wurin duba dajin Falgore dake Tudun Wada da karamar hukumar Doguwa da suke jihar Kano.

"Batun rashin jajircewa bai taso ba saboda jami'an tsaro sun shawarci mu hadu da Kano, Kaduna da jihar Bauchi don mu ga yadda zamu kawar da 'yan bindiga daga dajin Falgore.

"Na yarda da hakan amma gwamnonin jihar Kaduna da na Bauchi ba su je taron ba, sai dai suka turo wakilai.

"Akwai batun kudi. Gwamnatin jihar Kano, Kaduna da Bauchi sun tura kudadensu kuma ana sa ran hakan zai haifar da da mai ido.

"Ga alamu gwamnan bai gane yadda matsalar tsaro ba saboda ko wacce jiha da yanayinta," yace.

KU KARANTA: 'Yan sanda: Shanun da suka kutsa gidan Soyinka na wani bayerabe ne ba bafulatani ba

A wani labari na daban, Abduljabar Nasir Kabara, babban malamin da gwamnatin Kano ta haramtawa wa'azi ya maka gwamnatin jihar Kotu a kan tsaresa da tayi ba bisa ka'ida ba.

Gwamnatin Kano ta hana Kabara wa'azi a ranar 4 ga watan Fabrairun 2021 a kan zarginsa da wa'azi da zai iya tada zaune tsaye, The Cable ta wallafa.

A ranar 7 ga watan Fabrairu, gwamnatin jihar ta amince da mukabala tsakanin Sheikh Kabara da sauran malaman addini a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel