Sojin Najeriya basu son ganin karshen ta'addanci saboda suna amfana da shi, Sheikh Gumi

Sojin Najeriya basu son ganin karshen ta'addanci saboda suna amfana da shi, Sheikh Gumi

- Malamin addini Sheikh Ahmad Gumi ya zargi sojin Najeriya da ruruta wutar ta'addanci a kasar nan

- Kamar yadda ya tabbatar, ya ce sojin suna matukar amfana da biliyoyin kudin da ake warewa saboda yakar ta'addanci

- Ya ce 'yan bindiga sun shirya tsaf domin ajiye makamai amma sai za a gina musu makarantu, asibitoci da ruwan sha

Fitaccen malamin addinin Islama a arewacin Najeriya ya zargi rundunar sojin Najeriya da amfana da rashin tsaron da kasar nan ke ciki wanda hakan yasa basu son ta'addanci ya zo karshe sakamakon manyan kudaden da suke samu.

Sheikh Gumi, wanda yake ziyartar 'yan bindiga a dajika domin sasanci tare da tabbatar da zaman lafiya, a ranar Alhamis ya sanar da hakan yayin da aka yi hira da shi a Arise News.

"Rundunar sojin Najeriya bata bada kwarin guiwa wurin yaki da ta'addanci saboda tana matukar samu daga rashin tsaro," yace.

KU KARANTA: Alkali ya sabunta laifukan da ake zargin dan hadimin Tambuwal da wasu mutum 2

Sojin Najeriya basu son ganin karshe ta'addanci saboda suna amfana da shi, Sheikh Gumi
Sojin Najeriya basu son ganin karshe ta'addanci saboda suna amfana da shi, Sheikh Gumi. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

Kamar yadda Gumi yace, 'yan bindiga a shirye suke da su ajiye makamansu kuma su koma rayuwarsu kamar kowa idan gwamnatin tarayya za ta amince da kananan bukatunsu kamar gina musu makarantu, asbitoci da kuma samar musu da ruwan sha.

“Babu wanda zai goyi bayan laifi. Laifi dai laifi ne babu wata kalma da za a sakaya shi da ita. Amma ku duba IPOB, ba a taba sa rundunar soji sun sakar musu bama-bamai ba, tsagerun Niger Delta lallaba su ake yi," Gumi ya sanar da Arise News.

"'Yan bindiga suna korafin yadda sojin Najeriya ke kashe mutanen da basu da laifi. Hakan yasa suke siyan makamai. Amma ta ina suke samun makaman? Shine yasa suke garkuwa da jama'a.

“Idan aka duba za a ga sun shirya ajiye makamai kuma su koma rayuwarsu kamar kowa. Amma suna bukatar makarantu, asibitoci da ruwan sha.

“Akwai zargin da ake yi na cewa rundunar sojin bata so wannan rikicin ya kare saboda ana basu biliyoyin naira saboda yaki da ta'addanci. Hakan yasa basu bada hadin kan da ya dace.

“Ina jinjinawa 'yan sanda da sifeta janar na 'yan sanda. Ina jinjina musu yadda suka taimaka min na samu mutanen nan amma soji kuwa sai a hankali. Basu bada hadin kai," Gumi yace.

KU KARANTA: 'Yan sanda: Shanun da suka kutsa gidan Soyinka na wani bayerabe ne ba bafulatani ba

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce sun tattauna batun sauya sheka da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, daga jam'iyyar PDP ya koma jam'iyyar APC.

A wani bidiyo da aka daura a taron jam'iyyar APC da aka yi a jihar Kogi wanda aka saki a kafar sada zumunta ranar Laraba, Bello ya ce wannan yana daya daga cikin nasarorin da ya samu a matsayinsa na shugaban samari na kwamitin rijista da tabbatar da 'yan jam'iyya.

"Dan uwanmu kuma abokinmu, Chief Femi Fani-Kayode, ya koma jam'iyyar mu da kyakkyawan fata. Ya shigo jam'iyyar ne musamman don samar da cigaba wurin tabbatar da jam'iyyar ta bunkasa."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng