Miyetti Allah: Fulani sun yarda ayi wa duk Makiyayi rajista, za su fallasa 'Yan bindiga

Miyetti Allah: Fulani sun yarda ayi wa duk Makiyayi rajista, za su fallasa 'Yan bindiga

- Shugaban Kungiyar Miyetti Allah ya ce su na goyon bayan ayi masu rajista

- Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria ta ce su na da bata-gari

- Adamu Abache ya yi kira ga makiyaya su fallasa bakaken ashana a cikinsu

Shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN), na reshnen Ekiti, Adamu Abache, ya goyi bayan ayi wa makiyaya rajista.

Alhaji Adamu Abache ya yi kira ga gwamnatin jihar Ekiti, ta yi wa duk makiyayan da ke zama a Ekiti rajista domin aji dadin gane duk wani mai kiwon dabbobi.

Jaridar Vanguard ta ce Adamu Abache ya bukaci ayi wannan rajista ne a kananan hukumomin da makiyaya su ke zaune, su na kiwo ba tare da sun saba doka ba.

“Makiyaya da ke zaune a Ekiti su na neman zaman lafiya, kuma za mu cigaba da zama lafiya da wadanda su ka tarbe mu. Za mu cigaba da ba gwamnati goyon baya.”

KU KARANTA: Boko Haram: ‘Yan ta’adda sun yi mafaka a wasu Jihohin Arewa

Ya ce: “Gwamnati ta taimaka mana ta hanyar ba ‘yan kungiyarmu katin da za a rika gane mu, domin makiyaya su na fuskantar kalubale wajen bayyana kansu a jeji.”

“Dole gwamnati ta san inda mu ke, da inda mu ke harkokinmu, duk wanda ya yi wani laifi, za a iya damke shi, a mika shi a hannun jami’an ‘yan sanda.” inji Abache.

Abache ya yi kira ga mutanensa su tona duk wani makiyayi da ke yawo da makamai, ya na ta’adi. Shugaban kungiyar MACBAN ya ce yin hakan zai tsare mutuncin makiyaya.

Jagoran na Miyetti Allah ya ce idan ana bankado bata-gari da ke cikinsu ne za a gane cewa akwai makiyayan kwarai wadanda kiwo su ke yi, ba yi wa jama’a ta’adi ba.

Miyetti Allah: Fulani sun yarda ayi wa duk Makiyaya rajista, za su fallasa 'Yan bindiga
Gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi Hoto: @KFayemi
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kungiyar ACF ta na kukan babban banki ba ya yi wa Jihohin Arewa adalci

Alhaji Abache ya yi wannan bayani ne a lokacin da kwamitin ‘yan sanda da hulda da jama’a watau PCRC ya kira wani zama tsakanin duka kabilu a garin Ado Ekiti.

A jiya ne Bala Mohammed, gwamnan jihar Bauchi ya fito ya na cewa dole ce tasa makiyaya su ka dauki bindigogi, ya ce makiyaya basu da wata mafita illa su yi hakan.

Kamar yadda ya gwamnan na Bauchi ya fada, laifin duk aika-aikar da makiyayan su ke yi, ya rataya ne a wuyan gwamnati da al'umma da su ka gaza basu kariya.

Bala Mohammed ya caccaki gwamna Samuel Ortom a jawabinsa, maganar dai ta jawo ce-ce-ku-ce.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai (Info Mgt), kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel