Dattawa sun aika takarda ga Gwamnan CBN, sun ce ana cutar mutanen Arewa

Dattawa sun aika takarda ga Gwamnan CBN, sun ce ana cutar mutanen Arewa

- Arewa Consultative Forum (ACF) ta aika takarda zuwa ga Gwamnan CBN

- Kungiyar ta zargi babban bankin da ware jihohin Arewa a tsare-tsarensa

- Wasikar ta bayyana yadda ake cutar yankin ta manufofin tattalin arziki

Jaridar The Cable ta ce kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta dattawan Arewa, ta rubuta wasika zuwa ga gwamnan bankin CBN, Godwin Emefiele.

Kungiyar Arewa Consultative Forum ta koka wa gwamnan CBN a kan yadda ake ware jihohin Arewa wajen yin rabon tsare-tsaren tattalin arziki a Najeriya.

Shugaban ACF na kasa, Mista Audu Ogbeh ne ya sa hannu a wannan wasika da kungiyar ta aika.

Audu Ogbeh ya ce babu adalci, kuma ba a kyauta wa yankin Arewa a rabon da ake yi duk da cewa yankin ne ya fi kowane bangare yawan jama’a a fadin kasar.

KU KARANTA: Daga NYSC, Buhari ya ba zakakuran Matasa damar yin aiki da karo karatu

Tsohon Ministan gonan ya koka da cewa mutanen da ke zaune a karkara a yankin Arewa ba za su ci amfanin manufofin babban bankin kasar yadda ya kamata ba.

“Ba a duba kananan bankuna wadanda su ne ya kamata su amfani mafi yawan al’ummar kasar nan.”

“Wani sabon karamin banki guda wanda yake hannun gwamnati ne CBN ya ke tanka wa, ya raba kudin tallafi da shi, ana watsi da sauran kananan bankuna masu rajista.”

Wasikar dattawan Arewa ta kara da cewa: “Sauran kananan bankuna sai sun fita sun nemo kudi da tsada, sannan su yi takara da sauran bankunan da CBN ta ke fifita wa."

Dattawa sun aika takarda ga Gwamnan CBN, sun ce ana cutar mutanenn Arewa
Shugaban ACF, Audu Ogbeh Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Gwamnan Bauchi ya kare Makiyayan da ke yawo da makamai

Ogbeh ya kuma yi kaca-kaca da sabon sharadin da aka kawo wajen bude karamin banki, ya ce za a kori da-dama daga cikin bankuna 310 da ake da su a kaf Arewa.

A jiya Alhamis ne kuma shahararren Farfesan Ingilishin nan, Wole Soyinka ya jaddada cewa shi fa bai yarda shugaba Muhammadu Buhari ke mulkin kasar nan ba.

Farfesa Wole Soyinka ya ce bai yarda shugaba Buhari ne ke juya akalar gwamnatin Najeriya ba, sannan ya ce shugaban bai fahimci yadda sha'anin tsaro ya tabarbare ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai (Info Mgt), kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng