‘Yan Boko Haram sun kafa sababbin sansanoni, sun boye a Adamawa da Yobe
- Mayakan Boko Haram sun kafa sansani a Jihohin Adamawa da Yobe
- Jami’an tsaro sun samu labari wasu ‘Yan ta’adda sun fake a yankunan
- ‘Yan ta’addan su na gudun su yi artabu ne da dakarun sojojin Najeriya
Bayanan da jami’an tsaro su ke samu a Najeriya shi ne ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram sun kafa wasu sababbin sansanoni a Arewa maso gabas.
Jaridar Punch ta fitar da rahoto a ranar 11 ga watan Fubrairu, 2021, ta tabbatar da wannan lamari.
Rahoton ya ce ‘yan ta’addan wanda su ka shafe shekara da shekaru su na ta barna a yankin sun samu wasu mafaka inda za su rika boye wa jami’an tsaro.
Ana zargin cewa ‘yan ta’addan na kungiyar Boko Haram sun kafa wadannan sansanoni a yankin Geidam da ke jihar Yobe, da wani bangare a jihar Adamawa.
KU KARANTA: Babu abin da Buhari ya tabuka a kan tsaro - Ortom
Majiyar jami’an tsaro ta kuma bayyana cewa akwai yiwuwar ‘yan ta’addan sun tare a wasu garuruwan Yobe da su ka hada da Tarmuwa da Yunusari.
A jihar Adamawa kuwa, ‘yan Boko Haram sun fake ne a yankin Mubi, Madagali da kuma Gombi.
Karamar hukumar Madagali ta na kan iyaka ne da kasar Kamaru. A shekarun baya, ‘yan Boko Haram sun kai munanan hari a garuruwan Gombi da Mubi.
Ko a ‘yan kwanakin bayan nan, ‘yan ta’addan sun auka wa garin Geidam, su ka yi nasarar yin awon gaba da wasu jami’ai uku na hukumar kwastam na kasa.
KU KARANTA: Dattawan na Arewa sun ce Gwamnan CBN ya na cutar Jihohin yankin
‘Yan Boko Haram sun dauki akalla kimanin sa’a biyu su na ta’adi a karamar hukumar Geidam, mahaifar tsohon gwamnan jihar Yobe, Sanata Ibrahim Geidam.
Babban malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya zargi sojojin Najeriya da ruruta wutar ta'addanci a kasar nan, ya ce sun hana matsalar ta kare.
Sheikh Ahmad Gumi ya ce matukar jami'an tsaro su na amfana da biliyoyin kudin da ake warewa saboda yaki da ta'addanci, ba za a dage domin a samu tsaro ba.
Gumi yace 'yan bindiga sun shirya tsaf domin ajiye makamai amma bisa wasu sharuda.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai (Info Mgt), kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng