Buhari bai taɓuka wani abin azo a gani ba a fannin tsaro, in ji Gwamna Ortom

Buhari bai taɓuka wani abin azo a gani ba a fannin tsaro, in ji Gwamna Ortom

- Samuel Ortom, gwamnan jihar Benue ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya gaza a fanin tsaro

- Gwamna Ortom ya bada shawarar a kara mayar da hankali wurin tantance mutane da ke shigowa Nigeria

- Ortom ya kuma bawa Shugaba Buhari shawarar cewa ya kamata a sake nazarin dokokin zirga-zirga tsakanin kasashen ECOWAS

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bai tsinanawa yan Nigeria wani abin azo a gani ba a bangaren tsaro, The Punch ta ruwaito.

Ya yi kira ga shugaban kasar ya sake bita dokokin ECOWAS na zirga-zirgan mutane, hada-hadar kayayyaki da ayyuka a yankin Afirka ta Yamma.

Buhari bai taɓuka wani abin azo a gani ba a fanin tsaro, in ji Gwamna Ortom
Buhari bai taɓuka wani abin azo a gani ba a fanin tsaro, in ji Gwamna Ortom. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Tsohon gwamnan Zamfara, Yerima, ya gurfana gaban kwamiti kan zargin 'azabtar da ɗan kasuwa'

Ortom ya yi wannan kirar ne a Abuja a ranar Alhamis. Gwamnan ya ce makiyaya daga kasashen ketare suna amfani da damar da dokar ECOWAS din ta basu don shigowa Nigeria su janyo rikici.

Gwamnan ya ce, "Idan ba a saka dokar ta baci ba a kasar nan, za mu iya farkawa mu tarar babu kasar. Shugaban kasa ya gaza a fanin tsaro.

KU KARANTA: Jiragen yakin NAF sun sake halaka yan bindiga masu yawa a Kaduna

"A kasashen da muke makwabtaka da su kamar Ghana da Benin, ana binciken mutane sosai kafin su shiga kasashen. Ya kamata a rika bincika mutane sosai kafin a bari su shigo Nigeria. Yana nan cikin dokar ECOWAS, na yi nazarin sa, na ce lauyoyi na suma su yi nazarin.

"Mafi yawacin kashe kashen da ake yi ba yan Nigeria ke yi ba shima shugaban kasar ya fada haka da kansa yayin ziyarar da ya kai Hadaddiyar Daular Larabawa."

A wani labarin daban, Rundunar Sojojin Nigeria ta nada Mohammed Yerima a matsayin sabon direktan sashin hulda da jama'a, The Cable ta ruwaito.

Yerima, mai mukamin Brigedier-Janar zai maye gurbin Sagir Musa wanda ya kasance kakakin sojin na rikon kwarya tun shekarar 2019.

Kafin nadinsa, Yerima ya rike mukamin direktan sadarwa na tsaro da kuma mataimakin direkta a hedkwatar tsaro.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya tuntuɓarsa kai tsaye a shafinsa na Twitter @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel