Muna da sabbin dabarun yakar ta'addanci da 'yan bindiga a kasar nan, Osinbajo

Muna da sabbin dabarun yakar ta'addanci da 'yan bindiga a kasar nan, Osinbajo

- Mataimakin shugaban kasa Farfesa yemi Osinbajo ya ce an samu sabbin dabarun yakar ta'addanci

- Ya tabbatar da cewa sabbin hafsoshin tsaro da aka nada sun zo da hazaka tare da hanyoyin kawo karshen rashin tsaro

- Osinbajo ya ce suna mulkin kasar nan ne a lokacin da ake cikin manyan jarabawoyi na tsaro da annoba

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce nada sabbin hafsoshin tsaro da gwamnatin tarayya tayi yasa an samar da sabbin dabaru, hazaka da hanyoyin yakar ta'addanci, 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane a Najerya.

Osinbajo ya sanar da hakan ne a Ikenne da ke jihar Ogun a ranar Talata jim kadan bayan sabunta rijistarsa ta jam'iyyar APC, The Nation ta wallafa.

Mataimakin shugaban kasan yayi kira ga 'yan Najeriya da su gujewa duk wani yunkuri na tarwatsa hadin kan jama'a kuma sun yi aiki wurin tabbatar da shawo kan matsalar tsaro a kasar nan.

KU KARANTA: Hukumar EFCC za ta gurfanar da Sanata Oduah a kan zargin damfara

Muna da sabbin dabarun yakar ta'addanci da 'yan bindiga a kasar nan, Osinbajo
Muna da sabbin dabarun yakar ta'addanci da 'yan bindiga a kasar nan, Osinbajo. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

Ya ce, "Mu ne a gwamnati a irin lokacin nan me cike da kalubale. Annobar nan ta sake lalata abubuwa kuma muna fama da rashin saro.

"Dole ne mu tabbatar da cewa an damko masu garkuwa da mutane, 'yan bindiga da duk wasu nau'in rashin tsaro. Dole ne a yi adalci ta hanyar alaka mai karfi tsakanin 'yan sanda, ma'aikatun shari'a na jihohi da na tarayya.

"Da sabbin hafsoshin tsaron da muka samu, akwai sabbin dabaru, hikima da kuma hanyoyin kawo karshen ta'addanci a fadin kasar nan."

KU KARANTA: Ke duniya! Budurwa ta aika mahaifiyarta lahira bayan watsa mata tafasasshen ruwa

A wani labari na daban, shugaban rundunar sojin kasa, Manjo Janar Ibrahim Attahiru ya ce yana hango karshen artabunsu da Boko Haram a Najeriya nan babu dadewa.

Attahiru wanda ya fara aiki a ranar 26 ga watan Janairun 2021 ya sanar da hakan ne yayin da yake jawabi ga dakarun Special Army Super Camp Ngamdu a zagayesna na farko a Borno ranar Litinin, 8 ga Fabrairu.

Ya yi kira ga dakarun da su mayar da hankali wurin ganin bayan ta'addancin Boko Haram a kasar nan kuma su yi aiki domin dawo da zaman lafiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel