Hukumar EFCC za ta gurfanar da Sanata Oduah a kan zargin damfara

Hukumar EFCC za ta gurfanar da Sanata Oduah a kan zargin damfara

- EFCC ta gurfanar da Stella Oduah, tsohuwar ministan sufurin jiragen sama, bisa zarginta da satar kudade

- Ana zargin ta da wawurar kudade lokacin tana minista, yanzu haka Uduah sanata ce mai wakiltar mazabar Anambra ta arewa

- EFCC tana zargin Oduah da wawura tare da rub da ciki a kan dukiyar gwamnati lokacin tana minista

EFCC ta gurfanar da Stella Oduah, tsohuwar ministan sufurin jiragen sama bisa zargin wawurar kudaden al'umma.

An daga zaman da za a yi da ita ranar Talata saboda tsohuwar ministan bata nan.

Yanzu haka Uduah sanata ce mai wakiltar mazabar Anambra ta arewa, kuma ana zargin ta da wasu mutane 8 a wata kara mai lamba: FHC/ABJ/CR/316/20.

Hukumar tana zargin Oduah da kwasar kudin gwamnati lokacin tana minista, The Cable ta wallafa.

EFCC za ta gurfanar da Sanata Oduah a kan zargin damfara
EFCC za ta gurfanar da Sanata Oduah a kan zargin damfara. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ke duniya! Budurwa ta aika mahaifiyarta lahira bayan watsa mata tafasasshen ruwa

A ranar Talata lauyan EFCC, Hassan Liman, ya sanar da kotu cewa tsohuwar ministan bata riga ta shirya zuwa kotun ba, don haka ya bukaci alkali ya dage karar.

Kamar yadda yace, "Mai girma mai shari'a, yau ne aka gabatar da karar kuma na sanar da hukumar amma ba a riga an sanar da wacce ake kara (Oduah) ba.

"Sakamakon haka ne muke bukatar a dan daga shari'ar."

Iyang Ekwo, alkali mai shari'a yace aikin masu kara ne su gabatar da wanda suke kara gaban kotu. Don haka ya dage karar zuwa 22 ga watan Fabrairu.

KU KARANTA: Hotunan Auwalun Daudawa tare da mukarrabansu suna mika makamansu tare da tuba

A wani labari na daban, shugaban rundunar sojin kasa, Manjo Janar Ibrahim Attahiru ya ce yana hango karshen artabunsu da Boko Haram a Najeriya nan babu dadewa.

Attahiru wanda ya fara aiki a ranar 26 ga watan Janairun 2021 ya sanar da hakan ne yayin da yake jawabi ga dakarun Special Army Super Camp Ngamdu a zagayesna na farko a Borno ranar Litinin, 8 ga Fabrairu.

Ya yi kira ga dakarun da su mayar da hankali wurin ganin bayan ta'addancin Boko Haram a kasar nan kuma su yi aiki domin dawo da zaman lafiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel