Boko Haram: Ina hango karshen ta'addanci nan babu dadewa, Ibrahim Attahiru
- Shugaban dakarun sojin kasa, Manjo Janar Ibrahim Attahiru ya ce babu dadewa za su kawo karshen Boko Haram
- Kamar yadda ya bayyana a zagayensa na farko sansanin dakarun, babu dadewa za su koma cikin iyalansu
- Ya tabbatarwa da dakarun cewa nan babu dadewa za su samu isassun kayan aiki don ya ji kokensu daga kwamandojinsu
Shugaban rundunar sojin kasa, Manjo Janar Ibrahim Attahiru ya ce yana hango karshen artabunsu da Boko Haram a Najeriya nan babu dadewa.
Attahiru wanda ya fara aiki a ranar 26 ga watan Janairun 2021 ya sanar da hakan ne yayin da yake jawabi ga dakarun Special Army Super Camp Ngamdu a zagayesna na farko a Borno ranar Litinin, 8 ga Fabrairu.
Ya yi kira ga dakarun da su mayar da hankali wurin ganin bayan ta'addancin Boko Haram a kasar nan kuma su yi aiki domin dawo da zaman lafiya.
KU KARANTA: Son komawa wasa Turai domin gogayya da manyan 'zakaru' yasa na bar Al Nassr, Ahmed Musa
"Na san kun yi kokari a wannan yakin amma dole ne mu cigaba. Shugaban kasa ya san da aikinku kuma yana mika gasiuwarsa gare ku.
"Na samu ganawa da kwamandoji, sun yi min bayanin abubuwan bukata. Muna son kawo karshen wannan yakin nan babu dadewa. Kuna ganin nasarar da Operation Tura ta kai bango suke samu. Muna so mu cigaba har sai mun ga karshen yakin."
Shugaban ya tabbatar da cewa ba yankin arewa maso gabas ba kadai za su mayar da hankali, za su taba dukkan sassan Najeriya da rashin tsaro yayi katutu.
Ya tabbatar da cewa kalubalen suna da yawa amma za su dage ba kadan ba.
A bangaren abubuwan da suka shafi kayan aiki da sauransu, ya sanar da cewa an yi mishi bayani kuma sun kokartawa.
KU KARANTA: Alaka da 'yan bindiga: 'Yan sanda sun cafke tsohon shugaban karamar hukuma a Katsina
"A matsayina na shugaban ku, an sanar da ni matsalar kayan aiki. A cikin makonni kalilan masu zuwa zamu samar muku da khaki tare da kayan bada kariya. Ina hango mu mun bar wurin nan mun koma wurin iyalanmu," yace.
A wani labari na daban, kotun jihar Legas ta laifuka na musamman dake Ikeja ta yanke wa faston Living Faith Church wacce aka fi sani da Winner's Chapel, Afolabi Samuel, shekaru 3 a gidan gyaran hali bisa satar $90,000 da N4,500,000 wanda 'yan coci suka hada karfi da karfe suka tara.
EFCC ta gabatar da Samuel wanda shine akawu kuma ma'ajin cocin gaban alkali Mojisola Dada bisa laifuka biyu, almundahana da sata.
Kamar yadda EFCC ta gabatar, faston da wata Blessing Kolawole, wacce take aiki a jami'ar Covenant, sun hada kulle-kullen satar dukiyar kuma sun sake a aljihunansu don amfaninsu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng