Ke duniya! Budurwa ta aika mahaifiyarta lahira bayan watsa mata tafasasshen ruwa
- Wata mata ta rasa ranta a jihar Binuwai bayan diyarta ta watsa mata tafasasshen ruwan zafi
- Kamar yadda ganau suka sanar, fadan da ya kai ga watsa ruwan zafin an yi shi ne a kan omon wanki
- Matar ta mutu yayin da ake kan hanyar kai ta asibitin Makurdi sai kawai aka karasa da ita ma'adanar gawawwaki
Wani lamari mai matukar girgiza zukata tare da gigita jama'a ya auku a jihar Binuwai. Budurwa ce mai shekaru 18 ta zama silar mutuwar mahaifiyarta mai suna Mbachirin Ashiekaa.
Budurwar mai suna Winifred Ngutesen Ingyaji, 'yar asalin Ute-Tse-Kpun ce daga karamar hukumar Vandeikya ta jihar Binuwai.
Ta yi wa mahaifiyarta wanka da ruwan zafi wanda ya tafasa sannan ta raunata matar yayanta mai suna Jennifer Betsee.
KU KARANTA: Sabunta rijista a APC: Bata-gari sun aika da shugaban APC lahira a jihar Binuwai
Kamar yadda The Guardian ta wallafa, fadan ya fara ne tsakanin Winifred da matar yayanta mai suna Jennifer kamar yadda ganau suka tabbatar.
An kuwa fara fadan ne a kan omon wanki wanda ta siyo amma sai matar yayan ta dauka tayi amfani da shi.
A fusace Winifred ta dauka ruwan da Jennifer ke dafawa don yin wanka tare da jinjirarta.
A kokarin mahaifiyar Winifred na raba fadan, budurwar ta watsawa mahaifiyarta ruwan wanda hakan yasa aka kwasheta sai asibiti amma kafin a kai ta ce ga garinku.
A halin yanzu tana ma'adanar gawawwaki da ke asibitin Bishop Murray a Makurdi.
KU KARANTA: Ba za a iya jan ra'ayinmu don tabbatar da nadin da aka yi wa tsoffin hafsoshin tsaro ba, Majalisa
A wani labari na daban, fitaccen dan wasan kwallon kafa, Ahmed Musa mai shekaru 28 yana da dukiyar da ta kai $20 miliyan wanda ya samesu ta hanyar wasan kwallon kafa da tallace-tallace.
A yayin bayani a kan yadda babu zato balle tsammani ya bar kungiyar Al Nasssr da ke Saudi duk da tarihi mai kyau da ya kafa, Musa ya ce yana son komawa manyan gasa ne a Turai.
Da kan shi ya bukaci ya bar kungiyar kwallon kafan ta Riyadh duk da kuwa shekaru biyu ya kwashe daga cikin kwagilar shekaru hudu da yasa hannu. Ya sanar da ESPN cewa da kanshi ya mika bukatar barin kungiyar kuma yayi sa'a suka amince.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng