Ba za mu bari mutum 1 ya jawo mana rikici ba, Ganduje ya bayyana dalilin haramta wa Sheikh Kabara yin wa’azi
- Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya bayyana dalilin dakatar da wa'azin Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara
- Ganduje ya ce ba za su bari mutum daya ya jawo rikici a jihar da kalamansa ba
- Gwamnan ya kuma karyata ikirarin malamin na cewa akwai siyasa a cikin lamarin
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana ainahin dalilan da suka sa ya dakatar da Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara daga yin wa’azi da kuma bayar da umurnin rufe masallacinsa a Kano, tare da yin watsi da ikirarin malamin na cewa lamarin siyasa ce.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa ba za ta bari mutum daya ya jawo rashin zaman lafiya ba a jihar.
KU KARANTA KUMA: 2023: Malami ya karyata masu cewa fastocin kamfen dinsa na takarar gwamna sun bayyana
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa da yake zantawa da sashin Hausa na BBC a yammacin ranar Alhamis , gwamnan ya ce:
“Muna ta kallon ayyukansa a tsanaki. Jami’an tsaro na taka-tsantsan da abunda yake yi sosai kuma kun ga mun dauki mataki.”
“Yanzu muka fara, duba ga cewa abunda ya aikata zai kawo rashin zaman lafiya a Kano. Don haka jami’an tsaro na aikinsu don tabbatar da ci gaban zaman lafiya a Kano kuma ina fatan mutane za su fahimci hakan."
Kan dalilin da yasa gwamnati bata saurari ta bakin Kabara don yin sulhu ba, gwamnan ya ce:
“Ta yaya gwamnati ta watsar da shi? Bari na fada maku shi mayaudari ne, ta yaya gwamnati ta shiga wannan batu? Lokacin da ya kalubalanta da zagin malamai, shin gwamnati ce ta ce ya aikata hakan?
“Dalilin da yasa gwamnati ta shiga lamarin saboda yace duk mutumin da ya tunkari wajensa a yanka shi.”
KU KARANTA KUMA: Saurayi ya maka budurwa kotu bayan tura mata N5K amma taƙi zuwa ɗakinsa
Gwamna Ganduje ya ce hukuncin da gwamnatinsa ta dauka baya da nasaba da siyasa, inda ya kalubalanci malamin da ya ja da shi idan ya shirya.
“Karya yake yi cewa hukuncin na da nasaba da siyasa. Cewa yana umurtan mutanensa da su je suyi rijista, su je su yi. Akwai filin daga na siyasa, ya zo ya kara da ni ya ga abunda zai faru.
“Saboda ya tara wasu mutane suna tafa masa a koda yaushe sai Hakan na sa shi takamar cewa yana da mutane. Muma muna yin rijista a yanzu, bari mu ga wa zai yi nasara. Abkoda yaushe Allah na bayan masu gaskiya ne.”
Da yake martani ga ikirarin malamin na cewa kwamishinan ilimi na jihar ya gabbatar da cewa a tauye masa hakkinsa, Ganduje ya kalubalance shi da ya kawo hukumar cewa kwamishinan ya fadi abu makamancin wannan.
“Muna so ya kawo faifan murya inda kwamishinan fadi hakan idan ba karya yake yi ba. Abu na biyu mun ga bidiyo inda yace duk wanda ya je wurinsa a yanka shi. Wannan abu ne da ka iya kawo rikici kuma gwamnatin jihar Kano ba za ta bari hakan ya ci gaba ba."
A baya mun ji cewa Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya yi magana a kan dalilin da yake ganin shine ya sa gwamnatin jihar Kano ta dakatar da shi daga yin wa’azi.
A tattaunawarsa da jaridar Daily Trust bayan Gwamna Abdullahi Ganduje ya dauki wannan matakin a kansa, Sheikh Kabara ya yi zargin cewa matakin na da nasaba da siyasa ba wai addini ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng