Saurayi ya maka budurwa kotu bayan tura mata N5K amma taƙi zuwa ɗakinsa

Saurayi ya maka budurwa kotu bayan tura mata N5K amma taƙi zuwa ɗakinsa

- Wani mutumi a Kaduna ya haddasa cece kuce a shafin soshiyal midiya bayan ya maka wata budurwa a kotu kan saba yarjejeniyarsu

- Mutumin ya aika wa budurwar N5k kudin mota amma sai taki zuwa gidansa kamar yadda suka yi yarjejeniya

- Da aka kai lamarin kotun majistare, sai aka umurci bankin budurwar ya mayarwa da mutumin kudinsa a asusunsa

Wani mutum a Kaduna ya sa jama’a yamutsa gashin baki a shafin soshiyal midiya bayan ya kwato N5,000 da ya aikewa budurwa amma taki zuwa dakinsa kamar yadda suka yi yarjejeniya.

Mutumin ya kai lamarin gaban kotun majistare lokacin da budurwar taki zuwa dakin nasa sannan tayi ta basa uzuri mara kan gado, sai kotun ta umurci bankin budurwar da ya mayar masa da N5,000 dinsa.

Bankin yayi kamar yadda kotun ta umurta sannan aka mayarwa da mutumin N5,000 dinsa.

Saurayi ya maka budurwa kotu bayan tura mata N5K amma taƙi zuwa ɗakinsa
Saurayi ya maka budurwa kotu bayan tura mata N5K amma taƙi zuwa ɗakinsa Hoto: @Wizzfarukk
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Hukumar yan sanda ta sanar da kyautar N10m ga duk mutumin da ya iya bayyana inda wasu masu laifi suke

Da yake wallafa labarin a Twitter, shafin @Wizzfarukk ya rubuta:

“Wato mutumina ya aikewa wannan budurwa 5k don ta zo dakinsa daga Zaria zuwa Kaduna kawai sai ta fara bayar da wasu uzuri marasa kan gado sannan tayi kokarin yi masa yawo da hankali.

“Don takaita labarin kawai sai Baba ya dauki lamarin zuwa kotu sai aka mayar masa da kudinsa bisa umurnin kotu."

Jama’a sun je sashin yin sharhi don bayyana ra’ayinsu. Ga wasu daga cikin martanin.

@RealTalQ1 ya rubuta:

“Wasu lokutan ba wai kudin bane kawai manufar da ke tattare da shi ne. Ta karbi kudi bisa alkawarin kai masa ziyara, sai ta saba yarjejeniya shi kuma mutumin ya nemi a dawo masa da kudinsa...”

KU KARANTA KUMA: Shugaban Najeriya ya yabi Matasa, ya yi kira su yi koyi da shi a tafiyar APC

@Blackfranchiz ya yi martani:

"Wannan gayen sadauki ne."

A gefe guda, wata ‘yar fafutuka kare hakkin dan Adam a Najeriya Aisha Yesufu ta bayyana cewa ita ta jawo hankalin mijinta da kanta.

Aisha ta fadi haka ne a wata hira da tayi da BBC News Pidgin. Aisha uwa mai 'ya'ya biyu ta bayyana cewa ko yaushe tana bai wa mata shawara daga shekaru 30 zuwa sama da kada su jira har sai wani namiji ya zo ya latsa su kafin suyi aure.

A cewarta, mata suna zuwa wurin mazajen da suke so kuma suna neman aurensu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel