Sheikh Kabara: Ganduje ya hana mun yin wa’azi saboda na yi adawa da tazarcen shi

Sheikh Kabara: Ganduje ya hana mun yin wa’azi saboda na yi adawa da tazarcen shi

- An bayyana dalilin da yasa Gwamna Abdullahi Ganduje ya haramta wa Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara yin wa’azi a Kano

- Kabara ya yi zargin cewa hakan ya kasance ne saboda bai taba marawa gwamnan baya ba a zaben gwamna na 2019

- Malamin ya kara da cewa malamai da dama a jihar na aiki tare da gwamnati don adawa da shi

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya yi magana a kan dalilin da yake ganin shine ya sa gwamnatin jihar Kano ta dakatar da shi daga yin wa’azi.

A tattaunawarsa da jaridar Daily Trust bayan Gwamna Abdullahi Ganduje ya dauki wannan matakin a kansa, Sheikh Kabara ya yi zargin cewa matakin na da nasaba da siyasa ba wai lamarin addini ba.

KU KARANTA KUMA: Hawaye sun kwaranya yayinda tsohon dan majalisa Maikano Rabiu ya rasu

Sheikh Kabara: Ganduje ya hana mun yin wa’azi saboda na yi adawa da tazarcen shi
Sheikh Kabara: Ganduje ya hana mun yin wa’azi saboda na yi adawa da tazarcen shi Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Malamin ya ce gwamnan ya bi ta kansa ne saboda ya yi adawa da shi a lokacin zaben gwamna na 2019 a jihar.

“Dalilan a bayyane suke. Mutumin da ya dauki hukuncin (Ganduje) ya fadi lokuta da dama cewa baya yafiya.

“Na yi yaki da shi a lokacin zaben karshe da aka yi kuma ya yi alkawarin ramawa. Illa kawai ya dauki matakin da bai dace ba a lokacin da bai dace ba. Don haka wannan haramcin siyasa ce karara, bai da wani alaka da addini.”

Da yake kira ya mabiyansa kan su shirya kuri’unsu don zabe na gaba, Kabara ya ce ainahin makiyansa sune sauran malamai, ba wai gwamnati ba inda ya kara da cewa kawai dai a yanzu jihar na aiki ne a madadinsu.

KU KARANTA KUMA: Ko shakka babu yan Najeriya za su sake zabar APC a 2023, in ji Hope Uzodinma

A gefe guda, Sheikh Kabara ya ce rufe masallacinsa da hana shi yin wa'azo da gwamnatin jihar ta yi "zalunci ne", kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Malamin ya ce gwamnatin da kanta, ta bakin kwamishinan ilimi na jihar, ta tabbatar da cewa abinda ake yi masa zalunci ne amma ta dakatar da shi ba tare da bashi damar ya kare kansa ba.

Abdul-jabbar ya yi wannan jawabin ne biyo bayan rufe masallacinsa da ke makarantarsa da gwamnatin Kano ta yi a ranar Laraba gami da hana saka karuntunsa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta na jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel