2023: Malami ya karyata masu cewa fastocin kamfen dinsa na takarar gwamna sun bayyana
- Ministan shari’a, Malami, ya yi martani ga rahoton da ke ikirarin cewa fastocin kamfen dinsa na gwamna sun bayyana
- Ministan wanda yayi magana ta hadimin labaransa ya bayyana rahoton a matsayin karya tsantsa
- Sai dai kuma kakain Malami, Jibrilu-Gwandu, ya yarda cewa magoya bayan ministan a jihar na iya neman ya fito takara
Ministan shari’a Abubakar Malami, ya karyata batun cewa fastocin kanfen dinsa na gwamna sun karade unguwanni a jihar Kebbi.
A cewar jaridar Premium Times, hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga mai bashi shawara a kafofin watsa labarai, Umar Jibrilu-Gwandu a Birnin Kebbi a ranar Juma’a.
Mista Jibrilu-Gwandu na martani ne ga wani rahoton kafofin watsa labarai da ke nuna cewa fastocin kamfen din ministan na 2023 sun karade unguwanni a fadin jihar.
KU KARANTA KUMA: Duniya da faɗi take: Mijin Zahra Buhari ya caccaki matar da ta tsokanesa kan riga-kafin COVID-19
“An janyo hankalinmu zuwa ga wani rahoton karya da ke ikirarin cewa fastocin Atoni Janar na tarayya kuma ministan shari’a na neman kujerar gwamna a zaben 2023 sun cika ko ina a jihar.
“Mun karade birnin tare da yan jarida, sun gani da idanunsu cewa babu kamshin gaskiya a rahoton. Bamu ga kowani fosta makamancin haka ba a Birnin Kebbi.
“Don haka, muna so jama’a su yi watsi da wannan labari saboda hasashen mawallafin ne kawai,” in ji shi.
Mista Jibrilu-Gwandu ya bayyana cewa ministan na da magoya baya da dama a jihar da ka iya nuna ra’ayi a kansa, saboda taimakon al’umma da alkhairinsa, inda ya kara da cewa labarin fsatocin kamfen dinsa ba komai bane face kanzon kurege.
“A yanayi da wani zai shirya karairayi da sunan aikin jarida yana bata sunan aikin ne.
KU KARANTA KUMA: Saurayi ya maka budurwa kotu bayan tura mata N5K amma taƙi zuwa ɗakinsa
“Idan kun tuna, a ranar 16 ga watan Maris, 2020, Malami ya bukaci magoya bayansa da su janye daga batun kamfen din neman takarar gwamnansa na 2023, domin lokaci bai yi ba na kamfen din siyasa kamar yadda yake a dokar zabe na kasa,” in ji shi.
A gefe guda, gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya bukaci babban jigon jam’iyyar All Progressive Congress (APC), Bola Tinubu, da ya fuskanci wasu abubuwa masu amfani, inda ya bayyana cewa jam’iyyarsa da shi kansa ba za su ji kamshi shugabanci ba a zaben 2023.
Wike, ya baiwa Tinubu shawarar a ranar Alhamis, a Yola babbar birnin jihar Adamawa yayinda yake rangadi na wani aiki da Gwamna Ahmadu Fintiri ya aiwatar.
Ya ce da wadannan gagarumin kokari da gwamnonin Peoples Democratic Party (PDP) suka yi da kuma gazawar APC karkashin gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, yan Najeriya ba za su sake kuskuren zabar wata jam’iyya mara alkibla ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng