An yanke wa wasu mutane biyu hukuncin kisa bisa laifin fashi da makami

An yanke wa wasu mutane biyu hukuncin kisa bisa laifin fashi da makami

- Wata kotu a jihar Legas ta yankewa wasu 'yan fashi da makami hukuncin kisa

- Kotun ta gamsu da hujjojin da aka gabatar, kuma wadanda ake zargin sun amsa laifinsu

- Kotun ta yankewa wadanda ake zargin hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan amsa laifin

Wata babbar kotun jihar Legas da ke Ikeja ta yanke wa wasu mutane biyu, Moshood Ogunshola da Wasiu Lekan, hukuncin kisa ta hanyar rataya, jaridar Punch ta ruwaito.

An gurfanar da wadanda aka yanke wa hukuncin ne a gaban mai shari’a S.S Ogunsanya kan laifuka biyu da suka hada da hada baki da fashi da makami, wanda ya saba wa dokar shari’ar manyan laifuka ta jihar Legas.

KU KARANTA: Kiran dukkan makiyaya da sunan ‘makasa’ na iya haddasa yaki a kasar nan, in ji El-Rufai

An yanke wa wasu mutane biyu hukuncin kisa bisa laifin fashi da makami a wata jiha
An yanke wa wasu mutane biyu hukuncin kisa bisa laifin fashi da makami a wata jiha Hoto: Freedom Radio
Source: UGC

Mutanen sun amsa laifin da ake tuhumarsu da shi.

A cewar lauya mai shigar da kara, Adebayo Haroun, masu laifin sun yi wa wani mai suna Wasiu Rasaki fashin babur dinsa a yankin Ile Eja da ke Ikotun yayin da suke dauke da adda.

An tattaro cewa yan sanda sun cafke su sannan aka gurfanar dasu a gaban kotu.

Mai shari’a Ogunsanya ta same su da aikata laifin kuma ta yanke musu hukuncin kisa.

KU KARANTA: Daga kara masa wa'adi, IGP Adamu ya karawa wasu jami'ai girma

A wani labarin, Hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya ta ce wasu da aka gargame su 18 ne suka kammala karatun digiri daga jami'ar karatu daga gida ta National Open University ta Najeriya, BBC Hausa ta ruwaito.

A wata sanarwar da mai magana da yawun hukumar, Francis Enabore ya fitar a yau Alhamis ta ce tsararrun sun kammala jami'ar ne a fannonin karatu daban-daban.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel