Daga kara masa wa'adi, IGP Adamu ya karawa wasu jami'ai girma
- IGP Adamu ya yi karin girma ga wasu daga cikin jami'an 'yan sandan Najeriya ranar Alhamis
- IGP din ya yi wannan karin girma ne jim kadan bayan kara masa wa'adin watanni uku da akayi
- Rahoton ya bayyana sunayen jami'an da aka kara musu girma da kuma matsayin da aka basu
Sufeto-janar na ‘yan sanda, IGP Mohammed Adamu, a ranar Alhamis, ya nada babban jami’in sa (PSO), Idowu Owohunwa, da jami’in Ilimi na rundunar, Rabi Umar ado, matsayin kwamishinan ‘yan sanda a hedikwatar rundunar da ke Abuja, The Nation ta ruwaito.
Hakanan an yi nada ACP (Dr.) Adegbite Tunde Titus; ACP (Dakta) Chinonyerem Lawrence Welle da kuma Mataimaki na Musamman ga Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar, DSP Aderoju Olagunju, da sauransu.
Jami'an 'yan sandan da aka yiwa nadin suna daga cikin sabbin ayyukan hukumar 'yan sanda da aka daga darajar su, kamar yadda wata sanarwa daga kakakin rundunar 'yan sanda ta Najeriya @PoliceNG ta bayyana a shafin ta na twitter.
KU KARANTA: Kotu tayi watsi da tuhumar EFCC na badakalar N900bn kan tsohon gwamna Yari
Nadin na daga cikin ayyukan IGP din, wanda ya ci gaba da aikinsa bayan karin wa'adin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi, a jiya.
Wa’adin Adamu ya cika a ranar Litinin bayan ya kwashe shekaru 35 yana aikin dan sanda.
Amma Shugaban kasar ya sanar da kara wa’adin Adamu da watanni uku a ranar Alhamis.
Da yake sanar da hakan ga manema labarai na fadar shugaban kasa bayan ganawa da Shugaba Buhari, Ministan Harkokin ‘Yan Sanda, Muhammad Dingyadi, ya ce shawarar ta bayar da damar zabar wanda zai gaje shi ne ta hanyar da ta dace.
A cewar Ministan, Shugaban ya ajiye ikon kara wa'adin Sifeta Janar na 'yan sanda da watanni uku.
KU KARANTA: Kwamacala: Wata mata ta rabu da saurayinta ta kuma auri kanta
A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya tsawaita wa'adin Sifeto Janar na yan sanda, IGP Mohammed Adamu, da watanni uku.
Ministan harkokin yan sanda, Mohammad Dingyadi, ya bayyana haka ga manema labaran fadar shugaban kasa ranar Alhamis a Abuja.
Saurari karin bayani...
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng