Ci gaba: Wasu mutane 18 sun kammala digiri a gidajen kaso a Najeriya

Ci gaba: Wasu mutane 18 sun kammala digiri a gidajen kaso a Najeriya

- A kokarin ilmantar da wadanda ke daure a gidan kaso, National Open University ta yaye wasu dalibai

- An bayyana cewa daliban sun kasance a daure a gidan kason yayin da suke ci gaba da karatunsu

- A halin yanzu akwai da yawa cikin daliban a jami'ar, yayin da tuni an yaye 18 daga wasu gidajen kason

Hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya ta ce wasu da aka gargame su 18 ne suka kammala karatun digiri daga jami'ar karatu daga gida ta National Open University ta Najeriya, BBC Hausa ta ruwaito.

A wata sanarwar da mai magana da yawun hukumar, Francis Enabore ya fitar a yau Alhamis ta ce tsararrun sun kammala jami'ar ne a fannonin karatu daban-daban.

Sanarwar ta ambata yadda shugaban hukumar Mista John Mrabure ya taya su murnar kammala karatun sannan ya umarce su da su dauke shi a matsayin tubalin ginin rayuwarsu ta nan gaba.

KU KARANTA: Kotu tayi watsi da tuhumar EFCC na badakalar N900bn kan tsohon gwamna Yari

Ci gaba: Wasu mutane 18 sun kammala digiri a gidajen kaso a Najeriya
Ci gaba: Wasu mutane 18 sun kammala digiri a gidajen kaso a Najeriya Hoto: The Guardian
Asali: UGC

"Kusan 'yan gidan kaso 3,000 ne ke karatu a jami'ar Open University a yanzu haka, yayin da 50 ke karatun ilimin koyarwa na NCE a kwalejin Yewa da ke Jihar Ogun," in ji Francis Enabore.

Ya kara da cewa hukumar na da cibiyoyin karatu guda 12 a gidajen kaso da ke faɗin kasat ta Najeriya.

Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito cewa wani ɗan gidan kaso ne ɗalibi mafi hazaka a jami'ar Open University a shekarar 2014 daga gidan yari na Jihar Enugu, inda wani da yake daure ya sake cimma wannan matsayi a 2018 da gidan.

National Open University of Nigeria ta kasance jami'a ta farko da ake karatu ta yanar gizo. Jami'ar ta samu karbuwa a wajen 'yan Najeriya, yayin da a baya-bayan nan ta samu lasisi daga gwamnatin tarayya.

KU KARANTA: Kwamacala: Wata mata ta rabu da saurayinta ta kuma auri kanta

A wani labarin, Shugaban 'yan ta'addan da ke zaune a Zamfara, Turji, ya yi barazanar gayyatar mayaka 'yan kasashen waje don tayar da zaune tsaye a Najeriya, HumAngel ta ruwaito.

Wani shugaban ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, Kachalla Turji, ya ce kungiyarsa na iya yin kira ga goyon bayan kasashen waje don yaki da dagula Najeriya.

An ji Turji a cikin wani faifan bidiyo da aka yada a kafar Facebook suna tattauna korafe-korafen da suka ci gaba da kashe-kashe, satar mutane da kungiyoyin masu satar shanu a yankin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.