Kiran dukkan makiyaya da sunan ‘makasa’ na iya haddasa yaki a kasar nan, in ji El-Rufai

Kiran dukkan makiyaya da sunan ‘makasa’ na iya haddasa yaki a kasar nan, in ji El-Rufai

- Gwamnan jihar Kaduna ya bayyana cewa kiran dukkan makiyaya da makasa zai jawo yaki

- Ya bayyana cewa a kowace kabila ko addini ana samun mutumin kirki da na banza

- Yaa shawarci 'yan Najeriya da a hadu hannu wajen yakar wannan mummunan ta'addanci da kunno kai a kasar

Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya yi gargadi game da yiwa dukkan makiyaya kudin goro a matsayin masu laifi kuma masu kisan kai, The Nation ta ruwaito.

Ya ce yin hakan na da hadari kuma zai iya kunna rikici a Najeriya.

El-Rufai ya ayyana aikata fashi ya zama masana'anta kuma dole ne 'yan Najeriya su hada kai don kawo karshen sa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin karbar bakuncin shugabannin kungiyar Angilikan a Najeriya karkashin jagorancin Rebaran Henry Ndukuba.

KU KARANTA: Kotu tayi watsi da tuhumar EFCC na badakalar N900bn kan tsohon gwamna Yari

Danganta dukkan makiyaya da ‘makasa’ na iya haifar da yaki, in ji El-Rufai
Danganta dukkan makiyaya da ‘makasa’ na iya haifar da yaki, in ji El-Rufai Hoto: The Guardian News Nigeria
Asali: UGC

Ya ce akwai masu kyau da marasa kyau a cikin kowace kabila, yana mai bayyana 'yan Najeriya bai kamata ba, saboda ayyukan wasu 'yan kalilan masu aikata munanan ayyuka, sanya sunan duk wani kabila ko wata kungiyar addini da ta'addanci ba.

A cewar El Rufa'i: "Akwai lokacin da fashi da makami ya kasance keɓantattun mutane na wani yanki na ƙasar amma ba a taɓa bayyana su a matsayin ''kaza'' 'yan fashi da makami ne ba.

“Har ila yau, yaudara ta yanar gizo shima ya zama na musamman ga wasu yankuna na kasar amma ba a taba yiwa wata kabila lakani da Yahoo Boys ba.

“Wannan wani yanayi ne mai hatsari da zai iya kunna rikici a kasar nan. Akwai masu laifi daga cikinsu kuma dole ne mu gano su kuma mu magance su."

Ya kara da cewa: ‘’ Wannan rashin tsaro ya dabaibaye kasar nan. Kuma wasu 'yan bata gari suna kokarin amfani da shi don kara raba mu ta hanyar kabilanci da addini.

“Ra’ayinmu a nan jihar Kaduna shi ne, a kowace kabila, a kowane addini akwai mutanen kirki da kuma mutanen banza. Kuma aikinmu a matsayinmu na shugabanni shi ne gano mutanen da ba su dace ba kuma mu kama su kuma mu gurfanar da su a gaban kotu.”

KU KARANTA: Kwamacala: Wata mata ta rabu da saurayinta ta kuma auri kanta

A wani labarin, Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta sake ankarar da ‘yan Najeriya game da shirin da wasu mutane da kungiyoyi ke yi na haifar da rikicin kabilanci da addini a wasu sassan kasar.

Hukumar DSS a watan Junairu ta yi bayanin cewa wasu mutane suna aiki tare da mutanen waje don tayar da rikicin addini a fadin kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel