Gwamnan APC ya amince da hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane, rai da rai ga masu fyade
- Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu ya sa hannu akan wasu sababbin dokoki da hukunci a jiharsa
- Cikin dokokin har da hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da laifin garkuwa da mutane a cikin jihar
- Sannan ya amince da daurin rai da rai a gidan gyaran hali ga duk wanda aka kama da laifin fyade a jihar
Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu ya sa hannu bayan amincewa da sabbin dokoki biyar a jihar.
Kamar yadda takardar da Antoni Janar kuma Kwamishinan shari'a ta jihar, Hajiya Rahmatu Adamu Gulma ta gabatar ga manema labarai, tace Model Penal Code 2021 ta tanadar da hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da laifin garkuwa da mutane a jihar Kebbi a karkashin sashi na 247.
Sannan duk wanda aka kama da laifin yin fyade, karkashin sashin doka ta 259 yanki na 1, hukuncin daurin rai da rai ne.
Takardar ta kara da cewa Bagudu a watan Disamban 2020 ya amince da amsar kudaden haraji a jihar da kananun hukumomi dake fadin jihar Kebbi, The Nation ta ruwaito.
KU KARANTA: Jerin sunaye: Shugabannin dakarun sojin kasa na Najeriya tun daga 1999 da jihohinsu
KU KARANTA: Dan Najeriya ya gina katafaren gida da robobin lemu da ruwa cike da kasa (Hotuna)
A wani labari na daban, a ranar Alhamis, wani Keneth Okoro, mai shekaru 45 ya bayyana gaban kotun majistare dake Ikeja a jihar Legas, bisa laifin garkuwa da yaransa guda 2 wadanda suke hannun mahaifiyarsu.
Okoro bai amsa laifinsa ba da ake zargin ya aikata a ranar 19 ga watan Disamban 2020 a layin Atanda dake wuraren Mafoluku a jihar Legas, Vanguard ta wallafa.
Lauyan masu kara, Kehinde Ajayi, ya sanar da kotu cewa mutumin ya sace yarinyarsa mai shekaru 10 da dansa mai shekaru 8 da suke hannun mamarsu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng