Dan Najeriya ya gina katafaren gida da robobin lemu da ruwa cike da kasa

Dan Najeriya ya gina katafaren gida da robobin lemu da ruwa cike da kasa

  • Yahaya Ahmed, injiniya ne dan Najeriya wanda yayi amfani da gororin ruwa da na lemu wurin gina gida
  • Ahmed ya ce gidan karkonsa ya fi na bulo sau ashirin kuma zai iya yin shekaru 300 bai lalace ba
  • Injiniyan ya ce ya kirkiri wannan fasahar ne domin ya rage yawan gororin roba da ke lalata muhalli

Yahaya Ahmed injiniya ne dan Najeriya wanda ya gina gida da robobin ruwa da na lemu 14,800 da ya cika da kasa a Kaduna a matsayin bulk.

Premium times ta ruwaito cewa Ahmed darakta ne a wata kungiyar taimakon kai da kai mai suna Developmental Association of Renewable Energies in Nigeria (DARE).

Legit.ng ta gano cewa injiniyan ya ce da taimakon 'yan kungiyarsa suka gina gidan kuma sun yi hakan ne domin karfafa guiwar amfani da duk wasu nau'in kayan da za a iya sake amfani da su bayan an yi amfanin farko, samar da aikin yi da kuma tabbatar da muhalli mai kyau.

Kara karanta wannan

Muhammadu Sanusi II: Ina Tausaya Wa Wanda Zai Gaji Buhari

Dan Najeriya ya gina katafaren gida da robobin lemu da ruwa cike da kasa (Hotuna)
Dan Najeriya ya gina katafaren gida da robobin lemu da ruwa cike da kasa (Hotuna). Hoto daga @OfficialAHCN
Asali: Twitter

A yayin bayanin yadda aka gina gidan, Ahmed ya ce ma'aikata sun dinga cika robobin ruwan da na lemu da kasa kuma suka hada su kai da kai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce wannan ginin shine na farko irin shi da aka fara yi a Afrika kuma yana da matukar arha domin kuwa a titi ake tsintar kayan ginin ko kuma bola.

Gidan yana da dakunan bacci uku, bandaki da madafi. Ahmed ya ce ya fi gidan bulo karko sau ashirin kuma zai iya daukar shekaru 300 bai lalace ba matukar an gina shi yadda ya dace.

Kamar yadda yace, harsashi, ruwa da girgizar kasa basu iya yi wa gidan komai kuma zai iya jure sauyin yanayi kowanne iri.

Ahmed ya ce duk wanda ya iya gini zai iya gina irin wannan gidan kuma kungiyarsa ta horar da matasa masu tarin yawa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel