Jerin sunaye: Shugabannin dakarun sojin kasa na Najeriya tun daga 1999 da jihohinsu

Jerin sunaye: Shugabannin dakarun sojin kasa na Najeriya tun daga 1999 da jihohinsu

- An fara nada shugabannin dakarun sojin kasar nan tun a shekarar 1999

- An fara hakan tun daga kan shugaban kasa Olusegun Obasanjo har zuwa Muhammadu Buhari

- Laftanal Janar Buratai ne ya fi kowanne shugaban sojin kasan Najeriya dadewa a kujerarsa

An saba nada shugabannin tsaron kasar nan tun da aka fara mulkin farar hula a Najeriya. An fara hakan tun a shekarar 1999.

A jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sabbin hafsoshin tsaro a Najeriya kuma ya sallami wadanda ya fara da su tun daga 2015.

Ga jerin sunayen manyan hafsin sojin kasar nan da suka taba zama shugabannin dakarun sojin kasa a Najeriya:

KU KARANTA: Sai da 'yan daba suka fara harbe-harbe kafin su bankawa gidan Igboho wuta, 'Yan sanda

Jerin sunaye: Shugabannin dakarun sojin kasa na Najeriya tun daga 1999 da jihohinsu
Jerin sunaye: Shugabannin dakarun sojin kasa na Najeriya tun daga 1999 da jihohinsu. Hoto daga Channelstv.com, Thenationonlineng.net
Asali: UGC

Olusegun Obasanjo: Commander- in- Chief

Lt. Gen. Victor Malu (Benue): Mayun 1999 – Afirilun 2001

Lt. Gen Alex Ogomudia (Delta): Afirilun 2001 – Yuni 2003

Lt Gen Martin Luther Agwai (Kaduna): Yunin 2003 – Yunin 2006

Lt Gen Owoye Andrew Azazi (Bayesla): Yunin 2006 - Yunin 2007

Umar Musa Yar’adua: Commander in- Chief

Lt. Gen. Luka Yusuf (Kaduna): Yunin 2007 - Augusta 2008

Lt. Gen. Abdulrahman Danbazzau (Kano): Augusta 2008 – Satumban 2010

Goodluck Jonathan: Commander in chief

Lt. Gen. Azubuike Ihejirika (Abia): Satumban 2010 – Janairun 2014

Lt. Gen. Kenneth Minimah (Rivers): Janairun 2014 – Yulin 2015

Muhammadu Buhari: Commander- in- Chief

Lt. Gen Tukur Buratai (Borno): Yulin 2015 – Janairun 2021

Lt Gen Attahiru Ibrahim (Kaduna): Janairun 2021

KU KARANTA: Da duminsa: Alkalin farko na kotun daukaka karar Shari'ar Musulunci na jihar Kwara ya rasu

A wani labari na daban, Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya sanar da yadda wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bada umarnin kwace kudaden da ke bankuna na tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari.

Kudaden sun hada da wadanda ke bankunan Zenith da Polaris na kasar Najeriya, BBC Hausa ta wallafa. Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran ya ruwaito, kudaden da ke bankin Polaris sun kai dala hamsin da shida.

Akwai Naira miliyan 12.9, Naira miliyan 11.2, dala 30,309.99, Naira 217,388.04, dala 311,872.5 wadanda aka adana a bankin Zenith duk da sunan tsohon gwamnan da kamfanoninsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags:
NDA